Hukumar shirya zaɓe ta jihar Kaduna ta dage zaɓuka a ƙananan hukumomi 4 a jihar

0

LShugaban hukumar Zabe ta jihar Kaduna Sararu Audi-Dikko sanar da ɗage zaben kananan hukumomi a kananan hukumomi 4 a jihar.

Kananan hukumomin sun haɗa da na Birnin Gwari, Chikun, Kajuru da Zangon Kataf.

Audi-Dikko ta ce annyi haka ne saboda tsananin rashin tsaro da ake fama da shi a waɗannan ƙananan hukumomi.

” Jami’an tsaro da ke aikin samar da tsaro a sun tabbatar min cewa ba zai yiwu a iya gudanar da zaɓe a waɗannan ƙananan hukumomi ba.

” A dalilin haka ya sa gudanar da zabe a wadannan ba zai yiwu ba. Dole mu ɗage zaben saboda tsaron ma’aikatan da mutanen da za su fito zaɓe da kuma kayan aikin zaɓe.

Saboda haka hukumar ta ɗage zaben zuwa ranar 25 ga wannan wata ta Satumba.

A karshe ta yi kira ga mutane da su fito zaɓe cikin natsuwa da kwanciyar hankali.

Share.

game da Author