Ba ko’ina mutum zai yi noma ya samu yadda ya ke so ba. Haka lamarin ya ke ga Elizabeth Onyen, macen da ta kusa shafe shekaru 30 ta na noma.
Onyen ma’aikaciyar gwamnatin tarayya ce, amma yanzu ta yi ritaya. Ta fara shiga harkokin noma tun lokacin da aiki ya kai ta Jihar Gombe, har ta shafe shekaru ta na noma wake, shinkafa da masara.
Bayan ta daɗe ta na aiki a Gombe, an yi mata canjin wurin aiki zuwa Abuja, inda ta ke zaune a Kuje.
“Da aiki ya maido ni nan Kuje, ban yi gamo da katarin noma ba yadda na ke so, kamar yadda na riƙa samu a Jihar Gombe.
“A Gombe an samun manyan gonaki da za ka biya kuɗin aro ka noma shekara ɗaya.
“Sannan kuma a iyakar zama na a Jihar Gombe, ban fuskanci matsalar tsaro ba, har sai da na dawo Kuje tukunna.
“Tun farko dai na shiga noma ne saboda dalilai na samun wata kafar shigowar kuɗaɗe, bayan ɗan albashin da na ke ɗauka kafin lokacin.
“Sannan kuma akwai dalili na samun abincin da na ke iyar da iyalin mu. Don haka shi noma rufin asiri ne ba ƙarami ba.
“Na riƙa samun rufin asiri sosai da harkar noma a jihar Gombe. Amma a Kuje, tsawon shekaru huɗu kenan ina yin shuka, amma makiyaya na cinye min.
“Cikin 2017 na yi ritaya. Na maida hankali sosai ga noma, amma kuma sai na yi rashin sa’a makiyaya na tura shanu su na cinye min kakaf.” Inji Onyen.
“Na taɓa shuka masara sai bayan da ta fito ta yi yana ya sosai, makiyaya su ka tura shanu, su ka cinye baki ɗaya.
“Shekaru biyu da su ka gabata ma na yi dashen rogo a wata gonar da na karɓa aro. Ina ta murna rogo ya kama sosai. Wata rana miji na ya kira ni ya ce ga shi a gonar, amma makiyaya sun tura shanu duk sun cinye dogon baki ɗaya.
“Na tashi na bazama ni da ‘ya’ya na, sai mu ka iske ba ma ganyen rogon su ka cinye kaɗai ba, har da ainihin tushiyar rogon baki ɗaya.”
Onyen ta shaida wa wakilin mu cewa tun bayan dawowar ta Kuje, noma bai karɓe ta ba, amma matsalar ta makiyaya ce.
“Lokacin da na je na ga irin ɓarnar da aka yi mani shekaru biyu da su ka gabata, da na yi magana sai wani ɗan Bafulatani ya ce, “me za ki iya yi?”
Ta ce sana’ar da ta fi maida hankali a kan ta, a yanzu ita ce sana’ar sarrafa kayan abinci.
Ta yi ƙorafin ƙarancin jari da kuma rashin kayan noma na zamani. Ta ce ya kamata gwamnati ta riƙa tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi a fannin noma, musamman irin su mata, kuma waɗanda su ka yi rataya daga aiki.
Ta kuma yi ƙoƙarin cewa a kan nuna wa mata bambanci ko fifiko wajen wasu lamurra da su ka shafi harkokin noma a ƙasar nan.
Discussion about this post