Domin huce haushi da takaicin rashin samun aiki bayan ta kammala aikin bautar ƙasa (NYSC), sai Patience Dang ta rungumi harkokin noma gadan-gadan, daidai ƙwazon ta, kuma daidai ƙarfin ta.
Matar wadda ke zaune a Jos, babban birnin jihar Filato, ta rungumi noman masara da dankalin Turawa.
Ai kuwa ba ta daɗe da shiga harkar ba, sai ta yi kaciɓis da wata ƙungiya wadda ta tallafa mata har ta samu nasibi, buɗi da kuma yin tasiri sosai a harkar noman.
“Ni ban fi shekaru uku da fara harkar noma ba, bayan na kammala aikin NYSC ɗi na a Jihar Taraba.
“Bayan na dawo daga bautar ƙasa, na nemi aiki, amma na fahimci shi kan sa neman aikin ma wata wahala ce mai zaman kan ta. Sai kawai na yi tunanin fara noma kawai.
“Na fara da noma fili mai faɗin fuloti ɗaya da rabi. Sai da na karɓa aro na biya gonar. Mu na da gonar gado can a ƙauyen mu. Amma ni ba zan iya komawa can na zauna na yi noma ba. Kuma ba zan iya damƙa amanar a yi min noma ga wani a can, ni kuma ina daga nan ina tura masa kuɗi ba.
“Gona ta ba ta fi tafiyar minti 40 a ƙasa ba daga nan gida. Kuma wuri ne mai albarkar da har noman rani zan iya yi a ciki. Naira 25,000 na ke biya ladar aro a duk shekara.
“Na fara tarin kuɗaɗe tun ina jami’a. Amma a gaskiya ni ban taɓa tunanin zan yi noma ba. Ina tara kuɗi idan na je na yi ayyukan hidimar shirya taro an sallame ni. Kuma bayan na kammala digirin farko, na riƙa sayar da lemun Zoɓo ga wasu ma’aikatan haƙar ma’adinai.
“An tura ni Jalingo a Jihar Taraba domin yin aikin NYSC a can. To a Jalingo ɗin kuma na riƙa sana’ar sayar da kifi. Na kan je wajen masu kamun kifi na sayo na gyara su. Sannan na shanya su bushe. Daga nan ni ma sai na riƙa sayarwa a sassan ƙasar nan daban-daban ina turawa. Akwai ma lokacin da na ke sayarwa ga masu ‘supermarkets’ kawai a Taraba.”
Patience ta ce ba ta taɓa samun tallafi, lamuni ko ramcen kuɗaɗe ko kayan aiki daga gwamnati ba.
“Amma dai akwai wata ƙungiyar da ba ta gwamnati ba, mai suna Alluvial Agriculture, wadda a cikin 2020 na yi rajista da ita, ta hanyar wata ƙawa ta, bayan mun binciko ƙungiyar a Google.
“Bayan na yi rajista, sun yi mana bita sannan su ka nuna mana irin shuka na zamani mai saurin yin yabanya. Sannan ƙungiyar ta koya wa mata dabarun noma a matsayin ki na mace.
“Sun ba mu irin shukawa da kuma maganin kashe ƙwari, wanda na yi amfani da shi a gona ta wanann shekarar. Kuma ya na da inganci sosai. Kuma sun ba mu takin zamani. Akwai kuma wata ƙungiyar daban da ta ba mu tallafin kuɗaɗe.”
Patience ta ce da ya ke gonar ta ba mai girma ba ce, masu ƙwadago ta ke ɗauka su yi mata aikin gona. Ta ce wani lokaci kuma idan aikin ba mai wahala ba ne, ta na yin wanda za ta iya yi da kan ta.
Patience ta ce a kasuwannin ƙauye ta ke sayar da amfanin gonar ta.
“Amma ba ni sayar da dankalin Turawa. Ina barin sa ya yi yaɗo na riƙa sayar da irin sa kawai. Masara kuwa ba na fara sayar da ita sai cikin watan Yuni, saboda a lokacin ne ta fi tsada.”
Discussion about this post