HARE-HARE A MAKARANTUN AREWA: An yi garkuwa da ɗalibai 1000 cikin watanni takwas -Wata ƙungiya

0

Wata Ƙungiyar Fafutikar Ceton Ƙananan Yara mai suna Save the Children International, ta bayyana cewa ‘yan bindiga sun sace ɗalibai ƙananan yara fiye da 1,000 cikin watanni takwas a Arewa maso Yamma.

Ƙungiyar ta ƙara da cewa yawaitar kai farmaki da yin garkuwa a makarantu tsakanin 2020 zuwa 2021 ya haifar da rufe makarantu masu yawan gaske, lamarin da ya jefa harkar ilmi a halin taɓarɓarewa a yankin.

“Tsakanin watan Janairu zuwa Agusta, 2021, an sace ƙananan yara an yi garkuwa da su, waɗanda yawan su ya haura 1,000.

“Kuma har zuwa yanzu akwai ƙananan yaran da dama a hannun ‘yan bindiga a riƙe, an kasa biyan kuɗin fansar su.

PREMIUM TIMES Hausa ta sha buga labaran yadda mahara ke yawan satar ɗalibai a makarantun Arewa maso Yamma, a jihohin Kaduna, Katsina, Kebbi, Zamfara da Neja.

Waɗannan mahara sun arce da ɗaruruwan ɗalibai kuma ana ci gaba da biyan diyya.

Daraktan Ƙungiyar Sace the Children a Najeriya, Mercy Ghichuchi, ta yi wanann bayani a ranar Juma’a, ranar da aka ware domin zama Ranar Kare Ilmin Ƙananan Yara daga masu kai masa farmaki.

“Idan ya kasance ana kai wa harkokin ilmi barazanar hare-hare, to lamarin ya fi shafar ƙananan yara da ‘yan mata da manyan mata ne abin ya fi shafa.”

“Ana jefa yara ƙanana cikin halin ƙunci, tsoro, firgita, azabtarwa da kuma cin zarafin su.

“Yara da yawa a irin wannan lokacin ba su da wani zaɓi da ya rage, sai dai su ƙaurace wa neman ilmi kawai. Hakan kuwa na janyo su na asarar duk wani mafarki da muradin da su ke da shi na zama jiga-jigan al’umma ya fita daga tunanin su.”

Ghichuhi ta ce ƙungiyar ta ta damu sosai da yawaitar hare-haren da ‘yan bindiga ke kaiwa a makarantu kan ɗalibai, malamai da makarantun a Arewa.

Haka kuma wata ƙungiya mai suna GCPEA ta bayyana cewa tsakanin 2015 zuwa 2019 aƙalla an kai wa makarantun Boko 100 hare-hare a Najeriya.

“Hare-haren sun ƙaru sosai har sun yi matuƙar muni tsakanin 2020 zuwa 2021. Lamarin ya kai ga gwamnatocin jihohi sun rufe makarantun, saboda gudun kada ‘yan bindiga su kwashe yara ‘yan makaranta.

Save the Children International ta ce ƙasashen da harkar ilmi ta lalace sakamakon hare-hare sun haɗa da DRC Congo, Najeriya, Somaliya, Afghanistan, Sudan ta Kudu, Sudan, Mali, sai kuma Libiya.

Yayin da Syria da Yemen ke biye a baya.

Share.

game da Author