• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    Ƴan sanda sun ceto ƙananan yara 50 da aka kulle cikin kurkukun wani coci a ƙarƙashin ƙasa, a Ondo

    ‘Na sadaukar da rayuwa ta ga Najeriya’ – Inji sojan da mahara su ka kashe a harin Shiroro

    TA’ADDANCI A JIHAR NEJA: Yadda ƴan ta’adda su ka ratsa garuruwa, kafin su  kai wa sojoji da mobal farmaki

    Dalilin da ya sa ƴan bindiga ke ci gaba da kai wa mutane hari a jihar Neja – SSG

    JIHAR NEJA TA KAMA WUTA: Mahara sun kashe sojoji 30, mobal 7, farar hula da dama

    HARIN JIRGIN KASA: Ɗaya daga cikin waɗanda ƴan bindiga suka saki ta yi zanga-zanga a Kaduna

    Hasalallun Sanatocin APCn da su ka faɗi zaɓen fidda-gwani sun gana da Buhari

    Abubuwan da ya kamata a sani game da tsarin amfani da dabaru biyu wajen yin rajistar masu zabe – Nazarin DUBAWA

    INEC ba za ta rufe rajistar zaɓen 2023 a ƙarshen Yuni ba – Farfesa Yakubu

    Buhari ya rantsar da sabon Cif Joji na riƙo

    Teacher

    Gwamnati ta umarci makarantu su fara amfani da Tsarin Ƙara wa Malamai Shekarun Ritaya

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    LMC ta ci tarar Kano Pillars, ta kori shugabanta, Jambul bayan ya gobza wa ‘Rafiri’ naushi a haɓa

    Inganta Rayuwar Matasa Ta Hanyar Wasan Kwallon Kafa Da Gudunmawar Al’Ummah A Jigawa, Ahmed Ilallah

    CHAMPIONS LEAGUE: Ko dai tsinuwar Yaya Toure ta yi tasiri kan Pep Guardiola?

    PILLARS SUN KIRA RUWA: Daga yanzu a Abuja za su rika wasan gida kuma an zaftare musu maki 3

    Yadda Kanawa suka yi ragaraga da motar ƴan  Katsina United saboda Pillars ta buga kunnen doki a Kano

    GHANA vs NAJERIYA: Ko Najeriya za ta kauce wa ɗauko buhun kunya na 26 a hannun ‘Black Stars’?

    Barcelona ta yi wa Madrid dukan kabarin kishiya, ba sani ba sabo ta zura mata kwallaye 4 babu ko ɗaya

    ‘CHAMPIONS LEAGUE’: Yadda Benzama ya ceto Madrid daga rijiya gaba dubu, ya kori PSG kuma ya dawo da martabar sa a duniyar ƙwallo

    YAƘIN UKRANIYA YA CI ƘUNGIYAR CHELSEA: ‘Zan sayar da kulob ɗin na sadaukar da kuɗin ga tallafin waɗanda yaƙin Ukraniya ya kassara’ -Abramovich, mai ƙungiyar kuma ɗan asalin Rasha

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    HOTUNA: Ɗan Autan marigayi tsohon sarkin Kano Ado Bayero, Mustapha Ado Bayero, ya auri mata biyu ranar Asabar a  Kano

    BIDIYO: An yi wa ɗan takarar mu murɗiya a zaɓen fidda gwani na APC a Legas – Masu zanga-zanga

    KURUNKUS: Malami ya fito takarar gwamnan Kebbi, ya ce jama’ar jihar ne suka tilasta masa ya fito

    2023: Ɗan takarar shugaban kasa, Rotimi Amaechi ya ziyarci masarautar Dutse

    LABARI CIKIN HOTUNA: Yadda ƴaƴan jam’iyyar APC da dubban mutanen Kaduna suka yi wa Sanata Uba Sani goma ta arziki

    BIDIYO: Shin zaka iya zama da mai dauke da cutar Kanjamau? – Ra’ayoyin mutane

    Dalilin da ya sa muka yi tattaki har Dubai domin taya Aisha Buhari murnar zagayowar ranar haihuwar ta – Matan Gwamnonin Najeriya

    BIDIYO: Yadda ‘yan bindiga suka rika jibga ta kafin a biya naira 50,000 kudin fansa – Dattijo Saidu Dabo

    ‘Yan mata marasa aure sun fi matan aure amfani da magungunan takaita Iyali – Ma’aikatar Lafiya

No Result
View All Result

Hafsat Ganduje ta halarci saukar karatun autan ta a Landan, bayan babban ɗan ta ya kwance mata zani a kasuwa

Ashafa MurnaibyAshafa Murnai
September 15, 2021
in Manyan Labarai
0
Hafsat Ganduje ta halarci saukar karatun autan ta a Landan, bayan babban ɗan ta ya kwance mata zani a kasuwa

Hafsat Ganduje, matar Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano ta jibire wa gayyatar da EFCC ta yi mata, maimakon haka, ta garzaya Landan domin halartar bikin saukar karatun kammala digiri na ɗaya daga cikin ‘ya’yan ta.

Hafsat ta lula Landan daidai lokacin da Hukumar EFCC ta gayyace ta domin amsa tuhumar bincike, dangane da wani ƙorafin zargin danne wasu maƙudan kuɗaɗe da ɗan ta ya yi mata.

Harƙallar dai na da nasaba ce da daƙa-daƙar filaye a Kano.

A ranar Alhamis ce EFCC ta gayyaci Hafsat, wadda a Kano hatta mijin ta Ganduje ke kiran ta da laƙabin Gwaggo.

Ɗan ta Abdul’aziz Ganduje ne ya rubuta wa EFCC takardar ƙorafin cuwa-cuwar da ya yi iƙirarin mahaifiyar sa ta yi.

Sai dai kuma Kakakin Yaɗa Labarai na Gwaggo mai suna Abubakar Ibrahim ne ya bayyana tafiyar ta Landan a ranar Talata.

Dama kuma a ranar Talata an riƙa watsa hotuna da bidiyo mai ɗauke da Gwamna Ganduje, Hafsat Ganduje da wasu ‘ya’yan su tare da ɗalibin da ya kammala karatun na sa Landan.

“Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Matar sa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje da iyalan su, sun halarci bikin saukar karatun autan su Muhammad Abdullahi Umar Ganduje a Jami’ar Regent da ke Landan. Ya kammala digirin sa na farko, a yau Talata, 14 Ga Satumba, 2021.” Inji kakakin Gwaggo.

An dai gayyace ta domin ta halarci amsa tambayoyi a hedikwatar EFCC da ke Abuja a ranar Alhamis da ta gabata, amma ba ta je ba.

Ɗan ta mai suna Abdulazeez ne ya kai ƙarar ta Hukumar EFCC, inda majiya ta ce ya fallasa yadda Gwaggo ta tsoma yatsun ta cikin dagwalon dattin ruwan harƙallar filaye a Kano, domin ta ƙara azurta kan ta.

Dama shi ma Gwamna Ganduje ya shiga tsomomuwar zargin sunƙumen miliyoyin daloli a cikin aljifan babbar rigar sa, kamar yadda wasu faya-fayen bidiyon da aka bankaɗo su ka nuna shi.

Premium Times ta ji cewa Abdulazeez Ganduje ya ce shi aka ba kuɗaɗen ya damƙa wa mahaifiyar ta sa hannu da hannu.

“Amma bayan watanni uku sai mai neman filayen ya gano cewa duk da ya biya kuɗaɗen, bai samu filayen ba, an sayar wa wasu, sai ya nemi a biya shi kuɗin sa da bayar.” Haka wata majiya ta tsegunta.

An tambayi Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba, wanda ya ce ba shi da masaniyar hakan ta faru.

An kira lambar Kakakin EFCC Wilson Ewujeran, amma ba a same shi ba.

Wasu na cewa EFCC za ta iya aikawa a damƙe Gwaggo matar Ganduje, tunda ita ba ta da rigar kariyar tuhuma, kamar irin wadda mijin ta Ganduje ke da ita, a matsayin sa na gwamna.

Tags: AbujaGandujeHausaKanoLabaraiNajeriyaNewsPREMIUM TIMES
Previous Post

Manyan jami’an gwamnati ke sayen motocin da a ka yo sumogal ɗin su zuwa Najeriya – Hukumar Kwastan

Next Post

Nan da ƴan kwanaki kaɗan shafin Tiwita zai dawo aiki a Najeriya – Lai Mohammed

Next Post
Dalilin da ya sa gwamnatin Najeriya ta dakatar da Tiwita a Najeriya – Lai Mohammed

Nan da ƴan kwanaki kaɗan shafin Tiwita zai dawo aiki a Najeriya - Lai Mohammed

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • Ka zo ka yi mini mataimaki kawai – Kwankwaso ga Peter Obi
  • RIKICIN KWANCE WA ATIKU ZANI A KASUWA: Rundunar PDP ɓangaren Wike sun nemi a tsige Ayu, Shugaban Jam’iyya
  • YADDA KALLO YA KOMA OGUN: Obasanjo ya karaɗe Abeokuta ya na ɗaukar fasinja da Keke NAPEP
  • Ƴan sanda sun ceto ƙananan yara 50 da aka kulle cikin kurkukun wani coci a ƙarƙashin ƙasa, a Ondo
  • Mutum 77 sun kamu da Kanjamau a jihar Taraba

Abinda masu karatu ke fadi

  • Google on Masarautar Kano: Hassada Ta Sa Wasu Na Neman Wofintar Da Kokarin Su Danfodiyo! Daga Imam Murtadha Gusau
  • Kuşburnu Çekirdek Yağı on Dalilin da ya sa muka yi sallar Idi ranar Laraba a Bauchi, muka ki bin sanarwar Sarkin musulmi – Sheikh Dahiru Bauchi
  • Google on HARKALLAR BILIYAN 3.6: Ba nine Balan da ke jerin sunayen masu mallakin kamfanin Adda ba – Gwamna Bala
  • Google on SIYASAR ZAMFARA : Maitaimakawa tsohon dan takarar gwamna a APC akan harkar jarida ya sauya sheka
  • Google on RAMIN MUGUNTA: Yadda Boko Haram suka afkawa bam din da suka dana wa Sojojin Najeriya

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2022 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.