Gwamnatin Tarayya za ta ƙwato wasu miliyoyin da ta ce ta biya wasu likitocin Najeriya su 588 a bisa kuskure.
Wannan bayani na cikin tattaunawar da Ministan Ƙwadago Chris Ngige ya yi da manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa a ranar Litinin.
Ngige ya ce tun farko bai kamata a biya kuɗaɗen ga waɗancan ba’arin likitocin ba, domin kuɗaɗen na Gidauniyar Horas da Likitocin Ayyukan Ƙwararru ne, wato ‘Medical Residency Training Fund.’
Ya ce an bankaɗo sunayen likitocin da su cancanci karɓar kuɗaɗen ba, bayan an yi bincike a cikin sunaye 8000 da aka damƙa wa Gwamnatin Tarayya.”
Ministan ya ƙara da cewa wasu likitocin dai sun maida kuɗaɗen waɗanda aka biya su bisa kuskure, yayin da ake ci gaba da ƙara matsa-lambar ganin an karɓo sauran waɗanda su ka yi ragowar.
Ngige ya ce ɓata lokacin da likitocin ke yi wajen biyan kuɗaɗen waɗanda ba hskkini su ba, shi ya kawo tsaiko wajen biyan kuɗaɗen ‘Residency Fund’ da gwamnati ya kamata ta biya.
Yajin Aiki:
Da ya ke magana kan yajin aikin likitoci, Minista Ngige ya ce a shirye Gwamnatin Tarayya ta ke ta janye ƙarar da ta maka su a kotu, idan har su ka amince su ka janye yajin aiki, su ka koma bakin aikin su.
Sai dai kuma ya ce idan su ka ƙi komawa, to fa tabbas za a hana su albashin su, tunda ba su je sun yi aikin da ya cancanta su karɓi albashin ba.