Gwamnatin Tarayya ta raba kwanuka da cokulan cin abinci miliyan 1.2 a makarantun Kano

0

Gwamnatin Tarayya ta bayyana raba kwanukan cin abinci har guda miliyan 1.2 ga makarantun firamare a Kano.

Wannan shiri dai an ɓullo da shi ne domin inganta matakan tsaftace abincin da ‘yan makarantar ke ci da kuma nuna kulawa da lafiyar su.

Ministar Harkokin Agaji, Jinƙai da Inganta Rayuwar Marasa Galihu, Sadiya Faruk ce ta bayyana haka, a lokacin fara rabon kwanukan da aka yi a Makarantar Firamare ta Ƙwalli, wadda ke cikin birnin Kano.

Bashir Alƙali, Babban Sakatare na Ma’aikatar Jinƙai ne ya wakilci Minista Sadiya, a wurin fara rabon kayan, a ranar Laraba a Kano.

Shirin dai ya na gudana a ƙarƙashin Shirin Ciyar da ‘Yan Makaranta na Gwamnatin Tarayya, wato NHGSFP.

Sadiya ta bayyana cewa shirin wani haɓɓasa ne da Shugaba Muhammadu Buhari ke yi na raba kwanukan cin abinci ga ‘yan firamare a jihar Kano.

“Shirin HGSFP dai shiri ne na bayar da tallafi ga marasa galihu a ƙarƙashin NSIP, da nufin ƙara yawan ɗaukar ƙananan yara makarantun firamare, tare da inganta ba su abinci mai gina jiki.” Inji Alƙali.

Minista Sadiya ta ce zuwa yanzu gwamnati ta ciyar da yara ‘yan makaranta har miliyan 9, kuma ta ɗauki hayar mata masu dafa abinci har 100,000 a faɗin ƙasar nan.

Ta ce jama’a da yawa sun samu damar samun ayyukan yi a ƙarƙashin shirin ciyar da ɗalibai.

Tun da farko Gwamna Abdullahi Ganduje ya gode wa Shugaba Muhammadu Buhari da Minista Sadiya Faruk, bisa ƙoƙarin su na ganin ɗaliban Jihar Kano sun samu abinci mai gina jiki.

Share.

game da Author