Gwamnatin Tarayya ta ce za ta ɗaukaka ƙarar hukuncin tarar Naira biliyan 20 da Babbar Kotun Jihar Oyo ta ce sai ta biya gogarma Sunday Igboho.
Mai Shari’a Ladiran Akintola ne ya zartas da hukuncin, inda ya ce hukuncin zai zama darasi da kuma diyyar ɓarnar da jami’an tsaro su ka yi wa Sunday Igboho, a lokacin da aka kai wa gidan sa farmaki, a Ibadan.
Jami’an SSS ne su ka yi wa gidan dirar-mikiya a ranar 1 Ga Yuli.
Sunday Igboho dai ya nemi kotu ta tilasta Gwamnantin Tarayya biyan sa diyyar ɓarnar da aka yi masa, har Naira biliyan 500, a ƙarar da ya shigar kan Ministan Shari’a Abubakar Malami da kuma SSS.
Amma Malami ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya za ta ɗaukaka ƙara. Ya yi bayanin a lokacin wata tattaunawa da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), a ranar Juma’a.
Malami ya ce tuni an fara shirye-shiryen ɗauka ƙara.
Wani babban lauya mai suna Yomi Alliyu ne ya shigar da ƙarar a madadin Sunday Igboho, wanda a yanzu haka ke tsare a Jamhuriyar Birnin.
Mai Shari’a ya ce Gwamnatin Tarayya ta biya Sunday Igboho naira biliyan 20. Sannan kuma ta biya shi wasu Naira miliyan 2 matsayin kuɗin jeƙala-jeƙalar shigar da ƙara da Igboho ya riƙa yi, ta hannun lauyan sa.