Gwamnatin Kaduna ta dakatar da cin kasuwar mako-mako ta Kawo, ta hana safarar dabbobi daga jihar ko zuwa jihar

0

Kwamishinan tsaron jihar Kaduna Samuel Aruwan ya bayyana cewa Talatar wannan mako ce ta karshe da za a ci kasuwar Kawo dake cikin garin Kaduna.

Aruwan ya ce gwamnatin jihar ta dakatar da cin kasuwar ta mako-mako har sai kuma yadda hali ya yi.

Wannan sanarwa na kunshe ne a wata sanarwa da Kwamishinan ya fitar ranar Alhamis imda ya ƙara da cewa ba kasuwar ba kawai gwamnati ta hana safara dabbobi daga jihar ko kuma zuwa jigar daga ranar Alhamis din nan.

Idan ba a manta ba gwamnati ta dakatar da duka kasuwannin mako-mako a kananan hukumomi biyar a faɗin jihar.

Kananan hukumomin sun haɗa da Birnin Gwari, Chikun, Giwa, Igabi da Kajuru.

Wasu mazauna garin Kaduna kuma ƴan kasuwa dake kasuwancin nnsu a wannan kasuwa ta Kawo sun yaba wa gwamnati bisa wannan mataki da ta ɗauka suna masu cewa hakan da ta yi shine ya fi dacewa musamman a wannan lokaci da ake fama da matsalar tsaro.

Wani ɗan kasuwa mai suna Ɗanlami Bala ya ce ” Ina matukar farin cikin wannan abu da gwamnatin Kaduna ta yi, duk mai san’a a kasuwar Kawo ranar Talata ya san ba yadda aka saba ba ne ake yanzu musamman a cikin makonni biyu da suka wuce. Sabbin fuskoki da kaya masu yawa aka ruka shigowa da su ana siyarwa.

” Tunda aka rurrufe kasuwannin Zamfara da na wasu kananan hukumomin Kaduna dole ta Kawo ta zama cibiya ga kowa, wannan mataki yayi dai dai don tsaron mutane a jihar.

” Ni ma a nawa ra’ayin gwamnatin jihar ta yi daidai saka wannan doka, domin irin yadda muka ga kasuwar a makon jiya da wannan mako, akwai alamun tambawa a ciki. An rufe irin wadannan kasuwanni a Zamfara da wasu sassan jihar, sai ta Kawo ta zama ita ce babba a kewayen, haba irin cika da kasuwar ta yi gaskiya duk wanda ya saba cin ta duk Talata ya san akwai wani abu. Saboda haka gara a duba don tsaron talakawa. ”

Share.

game da Author