Gwamnatin Tarayya ta amince a kashe Naira biliyan 38.4, domin kammala wasu ayyukan titinan da aka bayar a lokacin gwamnatin Jonathan, amma ba a biya wasu kuɗaɗen ba, wasu ayyukan kuma ba a fara ba saboda rashin kuɗi a lokacin.
Minsitan Ayyuka da Gida Babatunde Fashola ne ya bayyana wa manema labarai haka, a Fadar Shugaban Ƙasa, bayan kammala taron Majalisar Zartaswa a ranar Laraba.
Fashola ya ce ayyukan titinan ba sabbi ba ne, duk waɗanda aka bayar da kwangilar su ne a lokacin gwamnatin Jonathan, amma ba a biya kuɗaɗen ba. Wasu kuma ko farawa ba a yi ba, saboda rashin kuɗi.
“Za a kammala ayyukan amma yawancin su duk sai da aka sake duba yarjejeniyar kwangilar, aka yi ƙarin kuɗaɗe, saboda tsadar kayan aiki tsakanin 2014 zuwa yanzu.”
Daga cikin titinan da Fashola ya bayyana, akwai aikin kilomita 13 a kan titin Anacha zuwa Owerri har ya dangana da Nnewi a jihar Anambra.
“An bayar da kwangilar tun cikin 2011, amma ba a biya kuɗin kwangilar ba. Yanzu an amince a biya domin a ƙarasa aikin, bayan an sake bibiyar kuɗaɗen aikin zuwa Naira miliyan 488,980,891.
“Sai kuma aikin titi mai tsawon kilomita 20 wanda ya haɗa da maida titin zuwa Yenagoa mai falan-biyu har zuwa Otuake.
“Tun cikin Disamba, 2014 Gwamnatin Jonathan ta bayar da aikin, amma ya samu tsaiko saboda hare-haren ‘yan takifen Neja-Delta da kuma ƙarancin kasafin kuɗi.” Inji Fashola.