Wannan ba hasashe bane, gaskiyace sai dai kuma wasu zai yi musu ɗacin gaske a baka.
Idan dai mutum ya shekara 50 zuwa ƙasa ba shi da hujjar nuna kiyayya ga gwamnatin Nasiru El-Rufai a jihar Kaduna sai dai kiyayya kawai na baya son sa don yayi masa wani abu da bai yi masa ɗaɗi ba.
Dole idan gyara ya zo wasu sai sun nuna ba su so, amma wannan gyara dole ne a yi shi kuma a so shi ko da ko za a haɗiyi zuciya ne.
Lallai za a iya yin kuskure a wasu wuraren hakan dole ne ayi su domin mutum bai cika 10 ba.
El-Rufai ya yi abinda ba a iya ganin inda ma yayi kuskure a Kaduna. Baya ga gyara fannin ilimin jihar da yayi, ya kusa musanya garin Kaduna kaf din sa, mutanen garin ba sai sun je Abuja ba, ko kasar Masar ko kuma birnin Landan kafin suga laftalaftar gadoji da manya tituna masu wutar lantarki a ko ina ba, suna haskawa kowa na al’amurorin sa babu tsangwama.
Babbar nasarar da ya samu wanda babu wata jiha da ta taɓa yin sa a kasar nan shine gudanar da zaɓukan kananan hukumomi da yayi.
Gwamna El-Rufai ne gwamna na farko da ya fara amfani da na’urar yin zabe mai amfani da ƙwaƙwalwa wanda abinda ka zaɓa shi zaka gani.
Yana gwamna amma bai saka baki a harkar zaɓen ba, ya faɗi rumfarsa amma kuma hakan bai sa wani abu ya canja ba.
Ya ci gaba da yin kira da ayi zaɓe cikin gaskiya da amana. Wace jiha aka taɓa yin haka? Babu. Gwamnoni sukan kasa abin su ne ko kun yi ko baku yi ba, jam’iyyar su da waɗanda suke so ke cin zaben ko anki ko an so, kuma babu wanda ya isa ya ce wani abu akai.
A wata jihar ma da abin ya gagara, wato gwamnan ya ga alaman zai iya shan ƙasa sai ya fasa yin zaɓen ya naɗa kantomomi.
Shi ko gogan na ka, wato guduma mai fasa kwarya, cewa yayi a fito a gwabza, duk wanda ya ci aba shi, sai ko ga ƴan Kaduna sun nuna masa halacci sun zaɓi jam’iyyar APC a dalilin sa duk da PDP ta ci wasu mazabun da kananan hukumomi.
El-Rufai dai yana aiki a Kaduna ne tsakanin sa da Allah, babu yaudara da nuna fifiko, idan ka yi da shi yayi da kai, idan ka yi watsi da shi, shima ya kama gaban sa ya rungumi talakawa ya ci gaba da rangaɗa musu aiki kawai, kai kuma sai ka je ka haɗiyi guduma, shi dai aiki ya kawo shi kuma ita ya sa a gaba.
Idan ka shekara biyu ba ka zo Kaduna ba dole sai an yi maka jagora a wasu hanyoyin in ba haka ba kuwa za ka yi ta zagaye ne kawai.
Baya muna furci don ya daɗaɗa ma wasu rai, abinda ya dace shi ake yi.
Fatar mu shine Allah ya kara masa lafiya ya sa a kai lafiya, kawo kuma karshin matsalar rashinntsaro da ake fama dadhi a kasar nan, Amin.
Mamman Yunus, manazarcin siyasa ne, mazaunin jigar Kaduna.
Discussion about this post