Ganganci ne buɗe wa ƴan bindiga wuta da gwamnati ke yi domin ƴan bindigan a shirye suke – Gumi

0

Fitaccen malamin addinin musulunci mazaunin garin Kaduna, Sheikh Gumi ya gargaɗi gwamnati da jami’an tsaro su janye daga kai wa ƴan bindiga hari domin hakan ba zai haifar wa kasa ɗa mai Ido.

Gumi ya bayyana cewa shi ya bisu har daji kuma ya san karfin makaman su, saboda haka darkake su da gwamnati ke kokarin yi fitina ne zai kawo wa kasa maimakon a samu zaman lafiya.

” An gwada fatattakar su ta tsiya amma ba a samu nasara ba sai ma taɓarɓarewar tsaro da aka samu. Yanzu idan aka ci gaba za su koma su nemi afkawa harkar ta’addanci kai tsaye, shike nan sai kuma a koma gidan jiya.

Ba tun yanzu ba Gumi yake kira da maimakon a darkake su, shi shawarar sa shine abi su ta lalama, a yi sulhu ne da su. Gwamnan Zamfara da Katsina sun rungumi wannan khuɗuba sai dai kuma bata amfanar da su da mutanen jihohin su ba domin karin azaba ne mutane suka dulmiya ciki daga ƴan bindiga, har dai suka janye daga wannan shawara ta malam.

Sace-sace yaran makaranta ya ƙaru, kashe-kashen mutanen da basu ji ba basu bani ya yawaita, gaba ɗaya komai ya dagule babu sauki.

Da yawa masu yin sharhi sun soki wannan shawara ta Sheikh Gumi cewa ba zai yiwu ana kashe mutane su kuma masu kidan kana bin su ka na lallaɓasu ba, sannan kuma ba ji suke yi ba. Hakan ma tunzura su yake yi.

Gwamnonin Kaduna da Neja sun turje cewa atitir ba za su zauna da ƴan bindiga ko su biya kudin fansar wanda suka sace ba.

Share.

game da Author