Fannin harkokin haƙo ɗanyen man fetur a Najeriya na neman faɗawa hannun wasu ‘yan gidogar da ke da kusanci da Shugaba Muhammadu Buhari, yayin da su ka tsoma dungulmin hannayen su wajen ganin an yi carafken daƙa-daƙa wajen naɗin Shugabannin Hukumomin Kula Da Ayyukan Haƙo Fetur wato ‘Upstream’, ‘Midstream’ da kuma ‘Downstream’.
Sabbin hukumoni ne guda biyu aka ƙirƙiro a ƙarƙashin Sabuwar Dokar Fetur (PIA), wadda Shugaba Buhari ya sa wa hannu kwanan farkon watan Agusta.
A Majalisar Tarayya da cikin ƙasa ana nuna damuwa ganin yadda waɗannan makusantan Buhari ke amfani da kusanci da shi, ba tare da sanin sa ba, su ke ƙoƙarin yi wa ɓangaren ‘Upstream’ kaka-gida, ganin cewa shi ne mafi muhimmanci a kan ‘Midstream’ da ‘Downstream’.
Ma’anar Hukumomin ‘Upstream’, ‘Midstream’ Da ‘Downstream’:
A ranar 16 Ga Satumba Shugaba Muhammadu Buhari ya sake aika wasiƙa ga Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, inda ya nemi a amince masa ya naɗa Shugabanni da Mambobin Hukumar Gudanarwa ga hukumoni biyu da su ka haɗa da:
1. Upstream Regulatory Commission.
2. Nigerian Midstream and Downstream Regulatory Authority.
Upstream Regulatory Commission na nufin Hukumar Kula da Ayyukan Haƙo Ɗanyen Man Fetur da Gas Daga Ƙarƙashin Ƙasa.
Nigerian Midstream and Downstream Regulatory Authority kuma na nufin Hukumar Kula da Sufurin Kayan Mai da Sarrafa Ɗanyen Mai Zuwa Fetur, Gas, Man Shafa, Giris, da sauran nau’o’in man da ake sarrafawa daga ɗanyen mai.
Yadda aka shigar da son zuciya wajen naɗa muƙamai:
Wasu ‘Yan Majalisar Tarayya su biyu sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa akwai damuwa sosai wajen yadda aka ƙudunduno sunayen shugabannin hukumomin aka gabatar, domin majalisa ta amince da su. Musamman idan aka yi la’akari da fannin da kowanen su ya fi ƙwarewa a kai, kafin a miƙa sunan na sa.
Birbiri da kan Jemage:
Sarki Auwalu, wanda a yanzu shi ne Daraktan Sashen Kula da Albarkatun Mai, inda ya ke da ƙwarewa da gogewar fiye da shekaru 20 a ɓangaren ayyukan haƙo ɗanyen mai (Upstream), sai aka bada sunan sa a matsayin wanda za a naɗa Shugaban Hukumar ‘Midstream’ da ‘Downstream’ Commission.
Shi kuma Gbenga Komolafe, wanda a yanzu shi ne Babban Manajan Harkokin Sayar da Ɗanyen Mai, aka bada sunan sa a matsayin sabon Shugaban Hukumar ‘Upstream’ Commission.
Masana kuma jami’an NNPC sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa Komolafe ya fi dacewa da Hukumar Midstream and Downstream Regulatory Authority, ba Upstream Regulatory Commission ba.
Wato dai kowanen su ya kawo gagarimin canji da ci gaba a muƙaman da su ke riƙe a yanzu. Amma kuma a wannan sabon naɗi, an kai kowa ba ɓangaren da ya dace a naɗa shi ba. An baddala su kenan.
Auwalu da Komolafe duk an naɗa su kan muƙaman da ba su dace da su ba. Inda ya kamata a naɗa Auwalu, sai aka naɗa Komolafe a wurin. Shi kuma Komolafe sai aka naɗa shi a kan muƙamin da ya dace a naɗa Auwalu.
Hakan da aka yi na nufin an naɗa kowanen su a kan fannin da kwata-kwata ba a kan sa ya ke da gogewa da ƙwarewa ba.
Yadda aka nunke Buhari baibai, aka baddala masa sunayen shugabannin:
Wata majiya ta ce, “shi dai Buhari na so a ɗora wanda ya cancanta a muƙamin da ya fi cancanta. Amma sai aka nunke shi baibai, kuma kai da ganin wasiƙar da ya aika wa Majalisar Dattawa, ka san an nunke shi baibai kafin ya rubuta wasiƙar ya aika.”
Yayin da aka kira ɗaya hukumar da sunan ‘Commision’, ɗayar kuma an kira ta ‘Authority’.
“Ganin yadda aka rufe wasiƙar da roƙon Majalisa ta amince a yi naɗin a “COMMISSION”, hakan zai sa Buhari ya yi tunanin cewa sunan Auwalu ne a Hukumar Upstream kenan.
Sabiu ‘Tunde’ Yusuf Da Abubakar Funtua: Makusantan Buhari da ke neman yi wa harkar Haƙo Fetur Kaka-gida:
Wannan ƙumbiya-ƙumbiyar dai an kitsa ta ne da hannayen Sabiu Yusuf, wanda aka fi sani da Sabiu Tunde, kuma wanda a yanzu ake ganin ya fi kowa kusanci da Buhari.
Ɗan-da-bai-san-yau-ba: Shi kuma wannan, wani Abubakar Funtua ne, ɗan marigayi Sama’ila Isa Funtua. Mahaifin sa kafin rasuwar sa, ya na ɗaya daga cikin na-kewaye-da-shugaban ƙasa.
Su biyun aka yi ittifaƙi da amannar cewa su na haɗa baki da wasu gaggan jami’an NNPC da kuma wani hamshaƙin ɗan kasuwa.
An yi zargi a iƙirarin cewa sun haɗa wani gungun masu ƙoƙarin ganin sun riƙa toya duk irin wainar da su ke son toyawa a Hukumar Upstream Regulatory Commission, wajen hada-hadar haƙo ɗanyen mai, kuma da dukkan harkokin mai a ruwa da tudu da gefen teku, tsakiya da cikin ruwa mai zurfin gaske.
Su na kuma son yin kaka-gida a al’amurran hada-hadar bayar da lasisin ayyukan da suka shafi haƙo ɗanyen mai da majiɓintan harkokin ɓangaren.
Majiya ta ce Sabiu ‘Tunde’ ba ya so ka naɗa Auwalu shugabancin Hukumar Upstream Regulatory Commission, saboda ba zai yarda ya miƙa wa ‘yan gidogar bori kan sa a yi masa girkar gada-gada, gidoga, handama, haɗama da asarƙala ba.
Kakakin Yaɗa Labaran Shugaban Ƙasa, Femi Adesina bai ɗaga wayar kiran da PREMIUM TIMES ta yi masa ba, ballantana a ji ta bakin sa.
Amma kuma wani jami’in da ke da kusanci da Ƙaramin Ministan Fetur, Timipre Sylva, ya ce ministan ya damu ƙwarai da wannan ƙalli-ƙalalla da makusantan Buhari ke shiryawa.
Sannan kuma ya ce babu wanda ya saka ministan ko neman shawarar sa wajen yin waɗannan naɗe-naɗe.
Haka kan shi ma Kakakin Yaɗa Labarai na Minista Sylva, Garbadeen Mohsmmed bai amsa kiran da aka yi masa ba, domin jin ƙarin bayani.
Sai dai Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa mai lura da Ayyukan ‘Upstream’, Sanata Phillip Aduda, ya ce kwamitin sa zai duba inda kowa ya fi cancanta ya zama shugaba, idan sun zo tantance sunayen, yayin da Auwalu da Komolafe su ka bayyana a gaban Majalisa domin amincewa da su.
Discussion about this post