FARAUTAR ‘YAN WASAN BRAZIL 4: Yadda Hukumar Daƙile Korona ta Tarwatsa Wasan Ajentina da Brazil

0

An dakatar da wasan neman hayewa zuwa Gasar Cin Kofin Duniya na Qatar 2022, minti huɗu kacal da fara fafatawa tsakanin Brazil da Ajantina a ranar Lahadi.

Jami’an Kiwon Lafiyar Brazil ne dai su ka kutsa cikin filin wasa na Neo Quimica Arena a birnin Sao Paulo da nufin damƙe ‘yan wasan Ajentina uku masu wasa a ƙasar Ingila, waɗanda su ka haɗa da Emiliano Martinez, Emiliano Buendia da kuma Giovani Ko Celso, sai kuma wani mai tsaron gida wanda ba ya cikin masu buga ƙwallo a lokacin, Cristian Romero.

An nemi damƙe su ne saboda sun karya dokar korona ta Brazil, wadda ta gindaya cewa duk wani mutum da ya shigo Brazil daga ƙasar Ingila, wajibin sa ne ya killace kan sa tsawon kwanaki 14.

Dokar na nufin dai waɗannan ‘yan wasa uku ba su cancanta shiga sitadiyan su buga ƙwallo ba, saboda daga Ingila su ka shigo, kuma ba su killace kan su tsawon kwanaki 14 ɗin da aka gindiya ba.

Alƙalin wasa Jesus Valenzuela daga ƙasar Venezuela ya yi ƙoƙarin kwantar da hankulan jami’an lafiya, ta hanyar ƙoƙarin hana jami’an.

Amma kuma ‘yan wasan ƙasashen biyu sun shiga kane-kane cikin husumar, domin kada rikici ko hargitsi ya tashi.

‘Yan wasan Ajentina sun fice daga filin wasa, su ka koma ɗakin da su ke canja kayan wasa.

Dokar Brazil dai ta ce duk wani wanda ya shiga ƙasar, muddin daga ranar da ya shiga zuwa kwanaki 14 a baya, idan dai ya shiga Ingila to sai ya killace kan sa tsawon kwanaki 14 a Brazil ɗin, kafin ya shiga jama’a.

Brazil dai ce kan gaba wajen fafutikar neman zuwa Cin Kofin Duniya na Qatar 2022 da maki 21.

Ajentina ke biye da ita, amma akwai ratar maki shida a tsakanin su.

Share.

game da Author