An tabbatar da mutuwar aƙalla mutum 10 tare da jikkata wasu mutum 20 a harin da Sojojin Jamhuriyar Nijar su ka kai wa ƙauyen Buhari.
Ƙauyen Buhari dai wani gari ne da ke da tazarar kilomita 20 daga Kananmma, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Yunusari ta Jihar Yobe.
Lamarin ya faru ne yayin da rahotanni su ka ce Sojojin Nijar sun afka garin ne lokacin da su ke farautar wasu ‘yan Boko Haram.
An kai harin ne jirgin yaƙi, inda aka kashe mutane da kuma jikkata wasu.
Ƙaramar Hukumar Yunusari na kan iyaka da Jamhuriyar Nijar.
Ganau ya ce da idon sa ya ga motoci uku ƙirar Toyota Hilux ɗauke da waɗanda aka ji wa rauni an shiga da su Babban Asibitin Geidam.
Wata majiya kuma ta tabbatar da cewa an garzaya da wasu Babban Asibitin Gashua.
Rundunar Sojojin Najeriya ta tabbatar da lamarin, kuma yanzu haka Sojojin Najeriya sun kewaye garin, sun hana jami’an tsaro shiga, cikin waɗanda aka hana ɗin kuwa har da ‘yan sanda.
Kakakin Yaɗa Labarai na ‘Yan Sandan Yobe, Dungus Abdulkarim ya ce ba su da cikakken bayanin haƙiƙanin abin da ya faru a zuwa lokacin da aka tuntuɓe shi.
A na sa ɓangaren, Gwamnan Yobe Mai Mala-Buni ya umarci asibitocin Geidam, Gashua da Damaturu su kula da lafiyar waɗanda aka jikkata a farmakin Ƙauyen Buhari kyauta.
Haka nan kuma ya umarci Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe ta gaggauta tura kayan tallafi ga jama’ar ƙauyen da abin ya shafa.
Sannan kuma ya bada umarnin jami’an gwamnati su yi aiki tare da jami’an sojoji domin a gano musabbabin farmakin.
Buni ya miƙa ta’aziyya da jaje da alhini dangane da wannan mummunan hari.