Gwamnan jihar Kaduna ya tabbatar wa tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II shugabancin jami’ar Kaduna a matsayin uban jami’ar.
An saka masa alkyabbar jami’ar da hula tabbatar da naɗin a wajen bukin yaye ɗaliban jami’ar da aka yi a Kaduna ranar Asabar sannan yayi jawabi da jagorantar bikin a matsayin sa na mai Jami’ar KASU.
Bayan haka a matsayin sa na shugaban jami’ar bayan naɗa shi sai ya jagoranci yaye ɗalibai da aka yi a makarantar.
Idan ba a manta ba, gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya naɗa sarki Muhammadu Sanusi uban jami’ar jihar Kaduna tun bayan cire shi da aka yi daga sarautar Kano.
.
Discussion about this post