Idan ba a manta ba a makon jiya, gwamnatin Kaduna ta saka dokar hana cin kasuwar mako-mako ta Kawo da ke Kaduna saboda aikin samar da tsaro da ake yi, sai dai kuma wannan doka bata yi tasiri ba.
Dubban masu siye da siyarwa sun halarci wannan kasuwa ranar Talata kamar yadda aka saba, sun kuma baje kolin su.
Wakilin PREMIUM TIMES da ya ziyarci Kasuwar ya ga dubban masu siye da siyarwa suna sha’aninsu, sai hada hada kawai ake yi ba tare da samun cikas ba.
Wasu da suka zanta da wakilin mu sun shaida cewa suna sane da dokar amma sun san ba zai yi tasiri ba.
” Na ji sanarwar amma na san ba tasiri zai yi ba . Ka ganni nan tun daga Zaria nake zuwa da kayan doya in kasa a wannan kasuwa.
Wani jami’in tsaro na sa kai ya bayyana cewa yazo kasuwar ne kamar yadda ya saba domin samar da tsaro. Ya ce shi ma bai ɗauka za aci kasuwar wannan satin ba.
Tun a makon jiya gwamnatin Kaduna ta sanar da dakatar da duka kasuwannin mako-mako a wasu ƙananan hukumomin jihar saboda tsaro.
Sanarwar wanda Kwamishinan tsaron jihar Samuel Aruwan ya fitar na kunshe da cewa hatta safarar dabbobi zuwa da fita daga jihar ya haramta daga yanzu.
Jihar Kaduna na daga cikin jihohi hudu a yankin Arewa Maso Yamma da matsalar rashin tsaro ya tsananta.
A cikin wannan makon, jami’an tsaron Najeriya sun nausa dazukan Zamfara inda suke ragargazar yan bindiga da yanzu haka suna can sun tattara nasu ina su neman mafaka saboda azabar da suke sha.
An kashe da dama daga cikin su, harda manyan su.
Discussion about this post