A ranar Talata ce Gwamna Rotimi Akeredolu na Jihar Ondo ya sa wa dokar haramta kiwo sakaka a fili a Jihar Ondo.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Donald Ojogo ne ya bayyana haka
Ojogo ya ce an sa wa dokar hannu bisa matsayar da Gwamnonin Kudu su ka cimma a wani taro da su ka yi a Legas.
A taro dai sun amince cewa kowa zai sa wa dokar hannu zuwa ranar 1 Ga Satumba, 2021.
“Kafa wannan doka na da muhimmanci sosai, domin za ta kawar da tashe-tashen hankula waɗanda idan akwai dokar, ba za a iya samun faɗace-faɗacen ba.”
Ya ce dokar za ta ƙara samar da zaman lafiya a Jihar Ondo.
“Ya kamata a fahimci cewa an kafa wannan doka ce domin samar da zaman lafiya da kauce wa kashe-kashen babu gaira babu dalili. Amma ba a kafa wannan doka don takura wa wani jinsi, ƙabila ko addini ba.”
Akeredolu ya sa wa dokar hannu bayan ƙudirin ya tsallake karatu na uku a Majalisar Dokokin Jihar Ondo, watanni uku da su ka gabata.
Ya sa wa dokar hannun a daidai lokacin da Ƙungiyar Kare Muradin Fulani ta Miyetti Allah ke adawa da kafa dokar.
Sauran jihohin da majalisar ta kammala karatun ƙudirin dokar sun haɗa Ogun, Osun, Oyo da kuma Ekiti.
Gwamnonin Kudu sun yi taro a Legas ranar 17 Ga Yuli, inda su ka amince za su kafa dokar haramta gararamba da shanu ana kiwo a jihohin su.
Sun amince za su sa wa dokar hannu zuwa ranar 1 Ga Satumba, 2021.
Discussion about this post