DALLA-DALLA: Dambarwar Dakatar Da Wasan Brazil vs Ajentina

0

1. ‘Yan wasan Ajentina 4, Emiliano Martinez, Emiliano Buendia, Cristian Romero da Lo Celso ne su ka kantara wa mahukuntan Brazil ƙarya cewa fiye da kwanaki 14 ba su cikin ƙasar Ingila.

2. Sun yi haka ne domin su samu iznin shiga ƙasar Brazil ba tare da sun bi ƙa’idar killace kan su ba, idan ba su daɗe da shiga Ingila ba.

3. An ankarar da ANVISA wannan karya doka da ‘yan wasan su ka yi, su ka shiga Brazil alhali ba su daɗe da barin Ingila ba.

4. ANVISA hukuma ce a Ƙarƙashin Ma’aikatar Harkokin Lafiyar Brazil, mai aikin daƙile cutar korona, tare da damƙe masu karya dokar korona.

5. Jami’an ANVISA tare da Rundunar ‘Yan Sandan Tarayya na Brazil sun garzaya otal ɗin da ‘yan wasan Ajentina su ka sauka, domin su kama ‘yan wasan huɗu. Amma sun taras har sun zarce sitadiyan, filin wasan su da ‘yan wasan Brazil.

6. Daga nan sai Gwamnantin Tarayyar Brazil ta tattauna da Hukumar Kwallon Ƙafa ta Brazil ,(CBF) da Hukumar Ƙwallon Kafa ta Latin Amurka (Conmebol), cewa su ɗage haramcin dokar a kan ‘yan wasan Ajentina ɗin, kuma aka amince.

7. Amma sai ANVISA ta ƙi yarda da ɗage wannan haramcin. Jami’an ta su ka garzaya sitadiyan domin su kamo ‘yan wasan 4.

8. Jami’an ANVISA sun ci karo da cinkoson motoci a kan titi, kafin su isa sitadiyan. Tuni kafin su isa har an fara taka ƙwallo.

9. Isar ANVISA da ‘Yan ke da wuya, sai su ka fara tattaunawa da jami’an CBF da na Conmebol, waɗanda su ka ce masu ai wasan an fara ba za a tsaida ba.

10. Amma ANVISA ta ce ai tilas sai dai a dakatar da wasan.

11. Daga nan jami’an ANVISA su ka tunkari jami’an ƙwallon Ajentina a gefen fili, yayin da ake ci gaba da wasa.

12. Bayan sun tattauna da jami’an ƙwallon ƙafar Ajentina (AFA), sai jami’an ANVISA da na ‘Yan Sanda su ka shiga fili, su ka samu alƙalin wasa, su ka dakatar da wasan.

13. Daga nan sai ‘yan wasan Ajentina su ka fice daga fili, su ka tafi ɗakin shaƙatawar hutun rabin-lokaci su ka yi zaman su.

14. Daga nan sai jami’an ANVISA da ‘yan sanda su ka yi ta ƙoƙarin ganin sun isa wurin ‘yan wasan 4 da su ke son damƙewa, su kuma duk sun shige cikin ɗakin shaƙatawa.

15. Daga cikin waɗanda wannan dambarwar ta ritsa da su, har da Leonel Messi na Ajentina da Neymar Jr. na Brazil.

Share.

game da Author