Dalilin da ya sa muka katse layukan sadarwa a kananan hukumomi 13 a Katsina – Masari

0

Babban mai ba gwamnan Katsina Aminu Bello Masari shawara akan Karkokin tsaro, Ibrahim Katsina ya bayyana cewa gwamnatin Katsina ta katse layukan sadarwa a wasu kananan hukumomi a jihar ne saboda ragargazar yan bindiga da ake yi a jihar Zamfara da kuma iyaka da suka yi da jihar Kaduna.

Sannan kuma an gano cewa wadannan mahara ke gudun neman tsira daga barin wutar sojojin Najeriya, za su iya fakewa a wasu kauyukan Katsina suna yin waya, saboda haka ne aka dode hanyoyin sadarwa a wurare.

Kananan hukumomin da aka katsewa layukan sadarwa sun hada da Sabuwa, Faskari, Dandume, Batsari, Danmusa, Kankara, Jibia, Safana, Dutsin-Ma Kurfi, Funtua, Bakori da Malumfashi.

Bayan haka, Masari ya hana wuraren saka cajin waye da ake biya a ko ina a fadin jihar, sannan kuma an dakatar da wasu manyan kasuwannin shanu a jihar da kuma masu saida man fetur a jarkoki.

Share.

game da Author