Daliban Kaduna za su koma makaranta ranar Litinin 13 ga Satumba

0

Kwamishinan Ilmin Jihar Kaduna Muhammed Shehu ya bayyana cewa za a bude makarantun jihar Kaduna ranar 13 ga watan Satumba bayan shafe watanni yara na gida.

Kwamishina Shehu ya fadi haka a taron marubuta harkokin ilmi da aka yi ta yanar gizo ranar Alhamis.

Kwamishina Shehu ya ce za a bude makarantun ne daga ranar Lahadi 12 ga wata, sai dai kuma ba za a koma domin karisa zangon karshe da dalibai ba su yi ba saboda rufe makarantun da gwamnatin jihar tayi.

” Za a koma makarantun Kaduna ranar 12 ga wata. Sai dai kuma za a fara sabon faifai ne wato zangon farko na sabon aji. Abinda ya rage a baya za a rika yin su ta yanar gizo har a karkare, amma sabon aji dalibai za su koma.

Share.

game da Author