A ranar Talata ne wani matashi ya bayyana wa rundunar Amotekun cewa ya an bashi naira 35,000 ya kawo kan mutum domin a yi amfani da shi wajen yin asirin kudancewa.
Rundunar Amotekun ta kama wannan matashi tare da wasu mutum biyu bisa zargin yanke kan wani tsoho mai suna Adeniyi Samuel mai shekara 73 a garin Ibadan.
Matashin ya ce bayan ya karbi kudin sai ya nemi wani mutum mai suna Alfa wanda ya kai shi wurin wani a kasuwar Bode amma sai mutumin ya ce ba zai iya siyar musu da kan mutum akan naira 35,000 ba.
” Bayan hake washe gari sai ga Alfa da wani tsoho, daga nan sai wuce da tsohon gidan sa ya danne shi kuwa ya yanke kan sa da takobi.
Shi kumu mutum na biyu ya bayyana wa rundunar cewa shine ya bai wa matashi na farko naira 35,000 ya kawo masa kan mutum.
Ya ce an kira shi a lokacin da Alfa ya ya kai wannan tsoho gidan sa kuma shine ya rike kafafuwan tsohon shi kuma Alfa ya yanke kan tsohon kamar ya kama dabba.
“Ina amsar kan sai na babbake shi domin tokar ake bukata wajen hada kolomboton da zai sa in kudance kafin awa 24. Kun ga gama tokar kan tsohon da na babbake a hannu na”
Shi kuwa Alfa ya ce ya dauko wannan tsoho a hanyar Amuloko a Ibadan.
Alfa ya ce da ya kawo tsohon sai ya kira wadannan matasa biyu inda suka taya shi kashe tsohon a cikin dakin sa.
Mataimakin kwamandan rundunar Amotekun Kazeem Babalola ya ce za su damka wadannan mutane hannun ‘yan sanda domin ci gaba da bincike.
Discussion about this post