Karamin ministan lafiya Olorunnimbe Mamora ya bayyana cewa macizai kan sari mutane akalla 20,000 duk shekara sannan akan rasa akalla mutum biyu wasu mutum kuma akalla 1700 na rasa wasu sassan jikinsu sabodsa dafin maciji da ya cije su.
Mamora ya fadi haka ne ranar Litini a taron wayar da kan mutane game da illar dafin maciji da aka yi a Abuja.
Taron ISBAD
A shekaran 2018 ne kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta tsayar da ranar 19 ga Satumba ranar wayar da kan mutane game illar dafin macizai a duniya.
WHO ta yi haka ne ganin yadda duk shekara adadin yawan mutanen da kan yi fama da sara ko dafin maciji na karuwa a duniyal.
Kungiyar ta ce macizai kan sari mutanen da basu da maganin kare kan su daga cizon macizai, talakawa, manoma, wadanda basu da ilimin boko da wadanda basu saka takalmi.
Sarar maciji a Najeriya
Mamora ya ce saran maciji matsala ne da ya dade yana cutar da lafiya da kashe mutane a kasar nan.
Ya ce macizai kamar su ‘Cobra or Naja nigricolis’, ‘Puff Adder’ or ‘Bitis arietans’ da ‘Carpet Viper or Echis ocellatus’ na cikin macizan da suka fi sarar mutane a kasar nan.
Maciji ‘Carpet Viper’ na cikin macizan dake saran akalla kashi 90% na mutane da kashi 60% na mutanen dake mutuwa a dalilin dafin maciji.
Mamora ya ce akan samu mutum 497 da maciji kan sara daga cikin mutum 1,000 a kasar nan.
“Bana an samu karuwa a yawan mutanen da macizai ke sara da yawan mutanen dake mutuwa da dafin maciji saboda yawan ruwan saman da aka samu a daminan bana.
Ya ce jihohin Gombe, Plateau, Adamawa, Bauchi, Borno, Nasarawa, Enugu, Kogi, Kebbi, Oyo, Benue da Taraba na cikin jihohin da suka fi fama da saran maciji a Najeriya.
Mamora ya ce Najeriya na cikin kasashen duniya da ta fi fama da matsalar saran maciji a duniya.
Sakamakon bincike ya nuna cewa mutum miliyan 5 ne maciji ke sara a duniya inda daga cikin mutum miliyan 2.5 kan yi fama da dafin maciji a duniya.
Binciken ya Kuma nuna cewa mutum 100,000 na mutuwa sannan mutum 300,000 kan rasa wani bangaren jikinsu saboda dafin maciji.
Babban sakataren ma’aikatar lafiya Mamman Mahmuda ya ce daga watan Janairu 2018 zuwa Disemba 2020 macizai sun sari mutum sama da 45,834 sannan mutum 1,793 sun mutum a Najeriya.