Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa da taimako da goyon bayan Amurka ne har Najeriya ke samun nasarar da ta ke samu yanzu a kan Boko Haram, inda ake ta daƙile su, su ke fitowa daga yankunan da su ke.
Yayin da Buhari ke ganawa da Wakiliyar Amurka ta Dindindin a Majalisar Ɗinkin Duniya, Linda Thomas-Greenfield, a Hedikwatar UN a New York a ranar Juma’a, Buhari ya ce goyon bayan da Amurka ke bai wa Najeriya ya ƙara wa Sojojin Najeriya ƙwarin guiwa sosai, kuma ya ƙara wa ‘yan ƙasar baki ɗaya yaƙinin samun nasara kan ‘yan ta’adda.
Yayin da Amurka ta fara turo wa Najeriya jiragen yaƙin da ta yi oda samfurin Tucano da kuma jiran wasu helikwaftocin yaƙi da ake yi, Buhari ya ce kakkaɓe matsalar tsaro a Najeriya zai iya yiwuwa nan da ɗan lokaci ƙanƙane mai zuwa.
Da ya ke magana a kan matakan da Najeriya ta ɗauka wajen hana korona samfurin “Delta” bazuwa, Buhari ya ce gwamnatin tarayya ta haɗa kai da jihohi wajen ganin an yi gagarimin shirin wayar da kan jama’a, lamarin da shugaban ƙasar ya ce ya yi tasiri sosai duk kuwa da yawan da ‘yan Najeriya ke da shi.
Da ta ke bayani, Jakada Linda ta ce kashi 70 bisa 100 na ayyukan da ta ke yi a Majalisar Ɗinkin Duniya duk ya maida hankali ne a ƙasashen Afrika.
Linda ta kuma nuna damuwa kan juyin mulkin da sojoji su ka yi a ƙasashen Mali da Guinea.