Tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma jigo a jam’iyyar PDP, Sule Lamido ya zargi manyan jam’iyyun Najeriya cewa duk ƴan gida daya ne bata sake zani ba, APCn ce ko PDP.
Lamido ya bayyana cewa ɗinbin matsalolin da ake fama da su a ƙasar nan sun samo asaline a dalilin rashin kishin ƙasa da ƴan siyasar ƙasar nan ba su da shi da kuma yadda bangaranci ya cika zuciyar mu.
Sule Lamido bai ɗaga wa jam’iyyar sa ta PDP kafa ba ita inda ya ce na jam’iyyar zai fi muni matuƙa idan ba a wancakalar da nuna bangaranci da son kai ba, an rungumi kishin kasa kuma an saka hakan a gaba-gaba.
” Mun fi maida hankali akan mulki kawai, mudai mu samu mulki, ba mu yin nazarin halin da ƙasa ke ciki da irin matsalolin ta. Haka APC ta yi a 2014, ta yi ta cika baki, za su yi wannan, za su yi wancan, babu abinda ba su ce ba. Yanzu ina muke? Lalacewar ba zai misaltu ba, kasa duk ta dagule.
” Idan PDP ba ta shiga taitayinta ba, muka ce siyasar ɓangaranci za mu yi, sai ɗan yanki na zai zama kaza, ba mu natsu mun yi abinda ya da dace ba, idan mulki ta dawo hannun mu, sai mun fi APC ragwargwaɓewa.
Duk da cewa jam’iyyar PDP ba ta faɗi yankin da ɗan takarar shugaban kasar ta zai fito ba, a ganin Lamido, a bari duk mai so ya baza kallin sa kawai, mai rabo da jama’a ya ɗauka.
” Idan ba a manta ba a 2014, na faɗi cewa da Atiku na PDP da Buhari na APC duk ba ƴan takarar da Najeriya za su yi alfahari da su bane idan ɗayan su ya yi nasara, dukkan su ba Najeriyar bace a gaban su kan su su ke yi wa.
Na faɗi cewa duka wanda ya yi nasara cikin su a zaben shugaban kasa, ba nasara ce ga Najeriya ba.
Discussion about this post