DAƘA-DAƘAR HUSHPUPPI: Buhari ne kaɗai ke da ikon damƙa Abba Kyari ga mahukuntan Amurka -Ministan ‘Yan Sanda

0

Ministan Harkokin ‘Yan Sanda Maigari Dingyaɗi, ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari kaɗai ke da ikon amincewa da buƙatar Amurka, inda ta nemi a damƙa dakataccen Shugaban Rundunar IRT, Abba Kyari.

Dingyaɗi ya jaddada haka a wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan Talabijin na Channels, a ranar Talata.

Wata kotun Amurka ce dai ta nemi a damƙa mata Kyari, domin binciken sa da kuma tuhumar sa, bisa zargin hannun sa cikin damfarar dala miliyan 1.1, wadda Ramon Abbas da aka fi sani da Hushpuppi ya ɗibga.

Wannan lamari ya kai ga Najeriya ta dakatar da Kyari, wanda Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda ne.

Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Usman Alƙali ne ya bada shawarar Hukumar Kula da Aikin ‘Yan Sanda ta dakatar da shi.

An dakatar da Kyari ne domin gudanar da bincike a kan alaƙar Abba Kyari da Hushpuppi.

Tun cikin makon jiya Premium Times ta buga labarin cewa kwamitin bincike ya kammala aikin sa, kuma ya miƙa rahoton sa ga Sufeto Janar Alƙali.

Sai dai kuma yayin da ya ke magana a kan batun Kyari, Dingyaɗi ya ce Gwamnatin Tarayya za ta tabbatar da cewa an yi abin da ya dace, kuma wanda ya cancanta a yi, saboda lamari ne da ya shafi ƙasa da ƙasa.

Ya ce rundunar ‘yan sandan Najeriya sun yi matuƙar ƙoƙarin ganin sun gudanar da komai a buɗe, babu wata ƙumbiya-ƙumbiya.

Minista Maigari Dingyaɗi ya ƙara da cewa kuma an damƙa wa Ministan Shari’a, kuma Antoni Janar na Tarayya, Abubakar Malami rahoton.

“Batun Abba Kyari ya karaɗe ko’ina. Kuma zuwa yanzu dai na tabbata kowa ya ji ‘yan sanda sun yi rawar-gani wajen kafa kwamitin bincike, wanda har ma ya kammala binciken sa. Kuma ya damƙa wa Sufeto Janar rahoton.

“Mun kuma damƙa wannan rahoto ga Ministan Shari’a, wanda zai yi nazarin sa, daga nan kuma ya ba Shugaban Ƙasa shawarar abin da ya fi cancanta a yi.

“Abin da ya kamata jama’a su fahimta, shi ne hukumar ‘yan sanda ta cika aikin da ya wajaba ta yi, wato kafa kwamitin bincike, wanda ya cika aikin sa.”

Share.

game da Author