• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    Buhari Travelling

    Duk da tsananin hare-haren da ya darkaki Najeriya a kwanakin nan Buhari zai waske taro Dakar

    An cika sansani uku fal da tubabbun ‘yan Boko Haram -Gwamna Zulum

    RUƊANI A APC: Gwamnan Neja, Bello ya ɗare kujerar Buni, Buhari ya bada umarnin Buni ya sauka daga shugabancin jam’iyyar

    IHU BAYAN HARIN SHIRORO: Gwamnatin Neja ta dakatar da haƙar ma’adinai a Shiroro, Munya da Rafi

    Barayi sun lalata tiransifoma 20 cikin makonni uku – Kamfanin Raba Wutar Lantarki

    SADAKA GUZURIN KIYAMA: Tsohon gwamnan da ya taya akanta jidar naira biliyan 84, ya yi wa malamai da ‘yan APC watandar shanu 370, ragunan layya 3,500 a Zamfara

    ZAƁEN GWAMNAN ANAMBRA: INEC za ta raba kayan aiki marasa hatsari daga Owerri

    ZAƁEN GWAMNAN OSUN: Matsalar tsaro da guguwar sayen ƙuri’u ne abin da ya fi damun mu -INEC

    Ƴan sanda sun ceto ƙananan yara 50 da aka kulle cikin kurkukun wani coci a ƙarƙashin ƙasa, a Ondo

    ‘Na sadaukar da rayuwa ta ga Najeriya’ – Inji sojan da mahara su ka kashe a harin Shiroro

    TA’ADDANCI A JIHAR NEJA: Yadda ƴan ta’adda su ka ratsa garuruwa, kafin su  kai wa sojoji da mobal farmaki

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    LMC ta ci tarar Kano Pillars, ta kori shugabanta, Jambul bayan ya gobza wa ‘Rafiri’ naushi a haɓa

    Inganta Rayuwar Matasa Ta Hanyar Wasan Kwallon Kafa Da Gudunmawar Al’Ummah A Jigawa, Ahmed Ilallah

    CHAMPIONS LEAGUE: Ko dai tsinuwar Yaya Toure ta yi tasiri kan Pep Guardiola?

    PILLARS SUN KIRA RUWA: Daga yanzu a Abuja za su rika wasan gida kuma an zaftare musu maki 3

    Yadda Kanawa suka yi ragaraga da motar ƴan  Katsina United saboda Pillars ta buga kunnen doki a Kano

    GHANA vs NAJERIYA: Ko Najeriya za ta kauce wa ɗauko buhun kunya na 26 a hannun ‘Black Stars’?

    Barcelona ta yi wa Madrid dukan kabarin kishiya, ba sani ba sabo ta zura mata kwallaye 4 babu ko ɗaya

    ‘CHAMPIONS LEAGUE’: Yadda Benzama ya ceto Madrid daga rijiya gaba dubu, ya kori PSG kuma ya dawo da martabar sa a duniyar ƙwallo

    YAƘIN UKRANIYA YA CI ƘUNGIYAR CHELSEA: ‘Zan sayar da kulob ɗin na sadaukar da kuɗin ga tallafin waɗanda yaƙin Ukraniya ya kassara’ -Abramovich, mai ƙungiyar kuma ɗan asalin Rasha

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    HOTUNA: Ɗan Autan marigayi tsohon sarkin Kano Ado Bayero, Mustapha Ado Bayero, ya auri mata biyu ranar Asabar a  Kano

    BIDIYO: An yi wa ɗan takarar mu murɗiya a zaɓen fidda gwani na APC a Legas – Masu zanga-zanga

    KURUNKUS: Malami ya fito takarar gwamnan Kebbi, ya ce jama’ar jihar ne suka tilasta masa ya fito

    2023: Ɗan takarar shugaban kasa, Rotimi Amaechi ya ziyarci masarautar Dutse

    LABARI CIKIN HOTUNA: Yadda ƴaƴan jam’iyyar APC da dubban mutanen Kaduna suka yi wa Sanata Uba Sani goma ta arziki

    BIDIYO: Shin zaka iya zama da mai dauke da cutar Kanjamau? – Ra’ayoyin mutane

    Dalilin da ya sa muka yi tattaki har Dubai domin taya Aisha Buhari murnar zagayowar ranar haihuwar ta – Matan Gwamnonin Najeriya

    BIDIYO: Yadda ‘yan bindiga suka rika jibga ta kafin a biya naira 50,000 kudin fansa – Dattijo Saidu Dabo

    ‘Yan mata marasa aure sun fi matan aure amfani da magungunan takaita Iyali – Ma’aikatar Lafiya

No Result
View All Result

CBN ya umarci bankuna su buga sunaye da lambar BVN ɗin masu harƙallar sayen dala

Ashafa MurnaibyAshafa Murnai
September 1, 2021
in Babban Labari, Harkokin Kudade/Noma
0
Bankin CBN ya rasa lakanin hana tsadar rayuwa ci gaba da yi wa talakawa kirbin-sakwarar-Ladidi

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya umarci dukkan bankunan kasuwanci su buga sunaye da BVN lambar waɗanda su ka sayi kuɗaɗen waje ta ɓarauniyar hanya.

CBN ya ce bankunan su buga sunayen a shafukan su na yanar gizo.

CBN ya fito da wannan umarni saboda samun rahotannin yadda wasu su ka riƙa sayen kuɗaɗen waje ta makauniyar kasuwa.

Sanarwar wadda Daraktan Kula da Sa-ido Haruna Mustapha ya sa wa hannu, tace wasu na yin harƙallar sayen kuɗaɗen waje ta hanyar samun bizar bogi ko kuma soke tafiyar ta su bayan sun karɓi kuɗaɗen canjin.

“Saboda haka CBN ta umarci bankuna su buga sunaye da BVN lambar kwastomomin da su ka yi wannan harƙallar.

Cikin watan Yuli ne CBN ya daina sayar da kuɗaɗen waje ga ‘yan canji.

Tun daga lokacin ‘yan canjin da CBN ke sayar wa dala 10,000 sau biyu a sati, sun riƙa dogara ne da bankunan kasuwanci domin ci gaban kasuwancin su.

Wannan ƙarancin Dala ya sa ta tsula tsada, har ta kai Naira 527 a ranar Talata.

Darajar naira ta ƙara zubewa bayan Bankin CBN ya hana sayar wa ‘yan canji kuɗaɗen ƙasashen waje.

Tun cikin wancan watan darajar naira a kasuwar tsaye ta ‘yan canji ta ƙara yin warsas a ranar da Babban Bankin Najeriya, CBN ya bada sanarwar daina sayar wa ‘yan canji dala da sauran kuɗaɗen ƙasashen waje.

A yanzu dalar Amurka ɗaya daidai ta ke da naira 505 a kasuwar ‘yan canji, kamar yadda shafin yanar gizon bayanan canji a Lagos, mai suna abokiFX.com ya nuna a yammacin ranar Talata.

CBN ya bada dalilai da yawa da ya sa ya daina sayar wa ‘yan canji kuɗaɗen ƙasashen waje, ciki har da zargin ana bi ta hannun su ana harƙallar karkatar da kuɗaɗe, lamarin da ke ƙara tauye tattalin arzikin ƙasa.

Bankin CBN ya daina sayar wa ‘yan canji kuɗaɗen ƙasashen waje, a ƙoƙarin da ya ce ya ke yi domin daidaita darajar naira da ta tattalin arzikin ƙasar nan.

Babban Bankin Najeriya CBN ya bada sanarwar daina sayar wa ‘yan canji kuɗaɗen waje kai-tsaye.

Shugaban Bankin CBN, Godwin Emefiele ne ys sanar da haka a ranar Talata a Abuja, bayan taron kwanaki biyu da Majalisar Tasarifin Tsare-tsaren Kuɗaɗe ta CBN ta gunadar.

Emefiele ya ce daga yau CBN zai riƙa sayar da dala d sauran kuɗaɗen waje ga bankunan kasuwanci kaɗai, ba ga ‘yan canji ba.

“Kuma CBN daga yau babu ruwan sa da shiga sha’anin yi wa kamfanonin ‘yan canji rajista.”

Ya ce wannan tsari da su ka ɗauka zai taimaka ƙwarai wajen ƙara wa naira ƙarfi da daraja a gaban idon kuɗaɗen ƙasashen waje.

CBN ya ce ya lura ana amfani da ‘yan canji ana karkatar da kuɗaɗen da ya kamata a ce an zuba su ne a jarin bunƙasa kasuwanci da tattalin arzikin cikin gida.

Daga nan sai ya ce duk mai son kuɗaɗen waje ya je wurin bankunan kasuwanci ya riƙa saye.

Sannan ya gargaɗi bankuna cewa duk wanda ya haɗa baki da ‘yan canji, za a yi masa hukuncin da sai ya yi da-na-sani.

Ya kuma gargaɗi ƙungiyoyin ƙasashen ƙetare waɗanda ya zarga da karkatar da kuɗaɗe ta hannun ‘yan canji, cewa su daina. Duk wanda aka kama, za a kai rahoton sa a gwamnatin ƙasar su.

PREMIUM ta buga labarin yadda wani masanin hada-hadar kuɗaɗe ya roƙi Bankin CBN ya rataya wa naira layar laƙanin hana ta firgita idan ta yi ido-biyu da dala a kasuwannin hada-hada.

Wani masanin ƙabali da ba’adin harkokin kuɗaɗe, Okechukwu Unegbu, ya roƙi Babban Bankin Najeriya (CBN) ya lalubo hanyoyin da zai saisaita tsadar kayan abincin da kayan masarufi ta hanyar dakatar da yawan farfaɗiya da faɗuwar ‘yan bori da naira ke yi a kasuwannin hada-hada na ciki da wajen ƙasar nan.

Okechukwu ya ce tsadar kayayyaki na ƙara tsananta cikin ƙasa, saboda darajar naira na ci gaba da taɓarɓarewa, sannan kuma a waje ko cikin gida duk inda naira ta yi ido-biyu da dala, sai ta fara karkarwa ta na firgita.

Okechukwu wanda shi ne tsohon Shugaban Ƙungiyar Mashahuran Masana Harkokin Kuɗaɗe na Cibiyar CIBN ta Najeriya, ya bada wannan shawara ce a ranar Lahadi, a wata tattaunawa da manema labarai a Abuja.

Ya ƙara da cewa yawan karyewar darajar naira da ake fuskanta abin damuwa ne, domin yanzu akwai wasu sinadarai da su ka kamata a yi amfani da su, wajen ƙara wa naira ƙarfi ta daina yawan firgita ko faduwar-‘yan-bori.

“Ya kamata Kwamitin Tsare-tsaren Ka’idojin Hada-hadar Kuɗaɗe na CBN ya yi nazarin shingayen da za a gindaya wa naira, matsayin kan iyakar da za a hana ta tsallakewa, kamar yadda bankin ya yi sau shida a baya.

“Har yanzu tsadar rayuwa da tsadar kayayyaki na hauhawa a Najeriya. Ƙuɗaɗen ruwan da bankuna ke bayarwa kuma sai hawa-da-sauka su ke yi. Sannan kasuwar canjin kuɗaɗen waje kuwa a nan ne aka fi yi wa naira laga-laga ko da kallo ta je, ballantana ta je cin kasuwar.

“Yanzu kusan naira 500 ce daidai da dala 1. A Najeriya idan ka na da naira 500, za ka iya cin abinci garau-garau har a jefa maka ‘yar tsokar nama. To inda tsiyar ta ke, idan ka je Amurka a can dala 1 babu abin da za ta yi maka.”

A ƙarshe ya bada shawarar cewa a yanzu da farashin ɗanyen mai ya yi sama a kasuwar duniya, ya kamata Kwamitin MPC na Bankin CBN ya bijiro da tsarin da zai samar da ayyukan yi sosai a ƙasar nan.

Tags: AbujaDalaHausaKuɗiLabaraiNewsPREMIUM TIMES
Previous Post

Babbar Kotu ta hana Gwamna ƙaƙaba dokar shiga masallatai da coci-coci da katin shaidar rigakafin korona

Next Post

Buhari ya kori ministan Noma Sabo Nanono da na Wutar Lantarki, ya yi sauye-sauye a wasu ma’aikatu

Buhari ya kori ministan Noma Sabo Nanono da na Wutar Lantarki, ya yi sauye-sauye a wasu ma'aikatu

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • KOWA TA SA TA FISSHE SHI: Ƙoƙarin haɗewar LP da NNPP ya kakare, Peter Obi zai bayyana mataimakin takarar sa ranar Juma’a
  • ‘Da gangar aka bari ƴan bindiga suka kai harin gidan yarin Kuje, saboda na yi ta faɗin hakan zai auku – Mamu
  • Ƴan bindiga sun babbake cibiyoyin kiwon lafiya sun yi dalilin dole aka rufe wasu 69 a Katsina
  • Dala ta ƙara kekketa wa naira rigar mutunci daidai lokacin tsadar kayan abinci
  • Duk da tsananin hare-haren da ya darkaki Najeriya a kwanakin nan Buhari zai waske taro Dakar

Abinda masu karatu ke fadi

  • Google on Masarautar Kano: Hassada Ta Sa Wasu Na Neman Wofintar Da Kokarin Su Danfodiyo! Daga Imam Murtadha Gusau
  • Kuşburnu Çekirdek Yağı on Dalilin da ya sa muka yi sallar Idi ranar Laraba a Bauchi, muka ki bin sanarwar Sarkin musulmi – Sheikh Dahiru Bauchi
  • Google on HARKALLAR BILIYAN 3.6: Ba nine Balan da ke jerin sunayen masu mallakin kamfanin Adda ba – Gwamna Bala
  • Google on SIYASAR ZAMFARA : Maitaimakawa tsohon dan takarar gwamna a APC akan harkar jarida ya sauya sheka
  • Google on RAMIN MUGUNTA: Yadda Boko Haram suka afkawa bam din da suka dana wa Sojojin Najeriya

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2022 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.