Naira na ci gaba da taɓarbarewa a kasuwar hada-hadar ‘yan canji, inda a ranar Alhamis ta jiya sai da dala ɗaya ta kai daidai da Naira 540.
Bincike da kuma bayanan musayar kuɗi a shafin abokiFX.com ya tabbatar da cewa an tashi kasuwar ‘yan canji da yammacin Alhamis dala ɗaya na daidai da Naira 540, tsadar da ba ta taɓa yin irin ta a baya ba.
Kusan watanni biyu kenan a kullum sai farashin dala ya ƙaru, darajar Naira kuma na durƙushewa.
A ranar Litinin sai da Dala 1 ta koma daidai da Naira 532.
Babban Bankin Najeriya (CBN) da Majalisar Tattalin Arzikin Najeriya sun kasa hana Naira taɓarɓarewa da sakwarkwacewar daraja da ta ke fuskanta a kasuwar ‘yan canji.
A ranar Litinin lalacewar darajar Naira ta kai ga ana sayar da Dala 1 Naira 532, zubewar darajar da naira ɗin ba ta taɓa yin irin haka ba, sai a ranar Litinin.
Naira ta ƙara durƙushewa a ranar Litinin zuwa 532 duk Dala 1, bayan da aka sayar da Dala 1 Naira 530 a ranakun Alhamis da Juma’a.
Tun a wancan makon wannan jarida ta buga rahoton yadda Dala ta yi wa Naira wanka da ruwan kwata a kasuwar ‘yan canji.
A yammacin ranar Labara an tashi kasuwar ‘yan canji bayan Dalar Amurka ta yi wa naira wanka da ruwan kwata.
A kasuwar bankuna a farashin gwamnati ma naira ta ci dukan tsiya bayan a ranar Talata ta fito ta na dukan ƙirji da kirari.
An tashi kasuwar ‘yan canji a ranar Laraba Dala 1 na daidai da naira 528, farashin da ba ta taɓa kaiwa ba.
Shugaba Muhammadu Buhari ya samu naira ta na daidai da Dala 1 naira 220, kuma dama kafin hawan sa mulki, ya yi alƙawarin zai daidaita naira daidai da Dalar Amurka.
A ranar Talata kuma an sayar da Dala kan naira 526.
Wannan tashin gwauron zabo da dala ke yi ya faru ne sakamakon ƙarancin ta a kasuwa.
Shi kuma ƙarancin ya faru ne sakamakon haramta sayar wa ‘yan canji, wato ‘Bureau de Change’ Dala kai tsaye da CBN ya daina yi.
Cikin wannan makon ne kuma CBN ya umarci bankunan kasuwanci su fallasa sunaye da lambar BVN ɗin duk wani wanda ya yi harƙalla da harigidon sayen dala ta makauniyar hanya a hannun su.
Tuni dai ake ɗora laifin karyewar darajar Naira ga Babban Bankin Najeriya (CBN), saboda ya fito da tsare-tsaren rage yawan Dala a hannun ‘yan canji, alhalin kuma ya kasa fito da matakan hana naira ci gaba da yin faɗuwar ‘yan bori.
Sagegeduwar CBN: Musabbabin Zubewar Darajar Naira:
Darajar naira ta ƙara zubewa bayan Bankin CBN ya hana sayar wa ‘yan canji kuɗaɗen ƙasashen waje.
Darajar naira a kssuwar tsaye ta ‘yan canji ta ƙara yin warsas a ranar da Babban Bankin Najeriya, CBN ya bada sanarwar daina sayar wa ‘yan canji dala da sauran kuɗaɗen ƙasashen waje.
A yanzu dalar Amurka ɗaya daidai ta ke da naira 505 a kasuwar ‘yan canji, kamar yadda shafin yanar gizon bayanan canji a Lagos, mai suna abokiFX.com ya nuna a yammacin ranar Talata.
CBN ya bada dalilai da yawa da ya sa ya daina sayar wa ‘yan canji kuɗaɗen ƙasashen waje, ciki har da zargin ana bi ta hannun su ana harƙallar karkatar da kuɗaɗe, lamarin da ke ƙara tauye tattalin arzikin ƙasa.
Bankin CBN ya daina sayar wa ‘yan canji kuɗaɗen ƙasashen waje, a ƙoƙarin da ya ce ya ke yi domin daidaita darajar naira da ta tattalin arzikin ƙasar nan.
Babban Bankin Najeriya CBN ya bada sanarwar daina sayar wa ‘yan canji kuɗaɗen waje kai-tsaye.
Shugaban Bankin CBN, Godwin Emefiele ne ys sanar da haka a ranar Talata a Abuja, bayan taron kwanaki biyu da Majalisar Tasarifin Tsare-tsaren Kuɗaɗe ta CBN ta gunadar.
Emefiele ya ce daga yau CBN zai riƙa sayar da dala d sauran kuɗaɗen waje ga bankunan kasuwanci kaɗai, ba ga ‘yan canji ba.