Tsohon ministan Sufurin Najeriya kuma jigo a jam’iyyar PDP a da, ya bayyana cewa yadda zai iya saka wa irin Nasarorin da gwamnatin Buhari ta samu kenan dawowa da jam’iyyar APC da yayi.
Idan ba a manta ba Fani-Kayode ya koma jam’iyyar APC a yau Alhamis inda bayan haka suka dunguma suka garzaya fadar shugaban kasa domin a yi masa wankar tsarki.
Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle, Sakataren gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha da Shugaban riko na jam’iyyar Mala Buni suka raka Fani Kayode fadar shugaban Kasa.
A jawabin da yayi wa manema labarai a fadar shugaban kasa, Kayode ya bayyana cewa ya dawo jam’iyyar APC ne saboda ya hada hannu da gwamnatin Buhari domin ci gaban Kasa.
” Buhari ya taka rawar gani a kasar nan musamman a fannin harkar samar da tsaro. Wannan ya sa dole ire-iren mu mu zo mu hadu wuri daya domin a ci gaba da samun nasara a abubuwan da gwamnati ta sa a gaba.
” Ita dama siyasa haka ta gada, duk inda kaga nan ne ci gaba ya karkata ga toh a matsayin ka na dan kasa, idan har kana da kishin kasa, sai ka zo a hadu wuri guda domin ci gaban kasar.
Gwamnan Yobe Mala Buni ya bayyana cewa, shugaba Buhari ya yi matukar Farin cikin wannan gagagimin kamun da APC ta yi.
Discussion about this post