Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa duniya fuska-biyu a Taron Majalisar Ɗinkin Duniya na 76 da ke gudana a birnin New York na Amurka.
A ranar Juma’a ce ya gabatar da jawabi a gaban shugabannin duniya, inda a cikin dogon jawabin na sa, ya roƙi manyan ƙasashen duniya su yafe wa ƙasashe marasa ƙarfi tulin basussukan da ya kumbura masu ciki.
Buhari ya yi wannan roƙo makonni biyu kacal bayan ya aika wa Majalisar Dattawa ta Najeriya wasiƙar neman amincewa ya sake ciwo bashin dala biliyan 4 da kuma fam na Ingila miliyan 710, kuɗaɗen da adadin su ya haura naira tiriliyan 2.
Dama kuma watanni biyu da su ka gabata, Majalisar Dattawa ta amince masa ya kinkimo bashin dala biliyan 8 da kuma wani na fam miliyan 490.
A jawabin Buhari a Majalisar Ɗinkin Duniya, ya ce yawancin wadannan basussukan da ƙasashen su ka ciwo, sun yi ne sanadiyyar karyewar da tattalin arzikin ƙasashen duniya ya yi sakamakon ɓarkewar cutar korona daga watan Janairun 2019.
Ya ce akwai matuƙar buƙatar a yafe wa ƙasashe masu tasowa da matalautan ƙasashe da kuma ƙasashen da ke kan tsibirai tulin bashin da su ka ciwo domin su samu su farfaɗo.
Haka kuma Buhari ya roƙi manyan ƙasashen duniya masu arziki da ke ƙarƙashin G20 su ɗaga wa ƙasashe masu tasowa lokacin da za su fara biyan basussukan da ke kan su.
Tuni dai a Najeriya ake ta ƙorafe-ƙorafen yawan basussukan da Gwamnatin Buhari ke yawan ciwowa.
Ko a cikin watan Agusta Kwamitin Lura da Kashe Kuɗaɗe na Majalisar Tarayya ya yi nuni da cewa yawan basussukan da ake ciwowa sun yi yawa.
Haka kuma a cikin wannan wata Sanata Ali Ndume ya yi kakkausan suka a kan yadda Buhari ke yawan ciwo bashi, amma babu wani abin kirki da za a iya nunawa a ce an yi da maƙudan kuɗaɗen.
A ci gaba da jawabin sa a UN, Buhari ya yi bayanin irin nasarorin da gwamnatin sa ta samu wajen daƙile matsalar Boko Haram, wadda a yanzu ɗaruruwan ‘yan ta’adda ke ta miƙa wuya su na sarauta tare da iyalan su.
Discussion about this post