BIDIYO: Yadda jami’in KASTLEA ya lakaɗawa wani direba dukan tsiya ya jefa shi ciki kwata a Kaduna

0

Wani jami’in hukumar KSTLEA ya rufe wani direba da dukan tsiya bayan kokuwa ya kaure a tsakanin su daga binciken takardun mota.

A wani bidiyo wanda wani Hosea Parah ya saka a shafin sa ta Facebook ranar Alhamis, an nuno jami’an KASTLEA din zagaye da wani direban mota, ɗaya daga cikin su da surfa masa ƙulli.

Kamar yadda yake a bidiyon jami’in KASTLEA din dai ga dukkan alamu ya fi karfi abokin fadar sa, hakan ya sa sai gwabgwabje masa baki ya rika yi, daga ƙarshe ma ya jefa cikin kwata ya kuma bishi ya ci gaba da surfarsa kamar ya samu gero.

Waɗanda suka tofa albarcin bakin su kan wannan bidiyo sun yi Allah wadai da wannan abinda wannan jami’i ya aikata.

” Yaya za ace wai mutumin da shine ya kamata ya hana amma kuma wai shine ya ke aikatawa , lallai shugabannin wannan hukuma su binciki wannan bidiyo sannan a hukunta waɗannan jami’ai.

Ita dai hukumar KASTLEA ta yi bakin jini sosai a jihar saboda irin waɗannan jami’ai da ba su daraja mutane.

Gwamnatin El-Rufai ta kafa hukumar ne domin su rika kula da hanyoyin jigar da direbobi dake bin hanyoyin.

Sai dai kuma, da yawa basu bin sharuɗɗan kada hukumar, abinda suka ga dama ne kawai suke yi.

Wasu sun yi kira ga gwamnatin jihar ta yi wa hukumar garambawul, a dauki wayayyu, waɗanda ke da ilimin da za su yi hulɗa da jama’a.

Share.

game da Author