Babban Jojin Najeriya ya mangari ƙeyar Manyan Alƙalai 7 da su ka yi shari’a sanye da rigar ‘yan siyasa

0

Babban Jojin Najeriya Tanko Muhammad, ya bayyana cewa Ma’aikatar Shari’a ba za ta zura idanu rashin ɗa’a ko wasu alƙalai ‘yan damaga su zubar da ƙimar shari’a ba.

Cif Jojin ya yi wannan gargaɗin a ranar Litinin a Abuja, yayin da ya yi ta faman zaman ganawa da wasu Manyan Alƙalan Jihohi su bakwai, waɗanda su ka riƙa bayar da hukunci ga shari’un da ke da nasara da siyasa a duƙunƙune.

Cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na Kotun Ƙoli, Soji Oye ya fitar a ranar Litinin, ya ce Babban Jojin Najeriya ya fara ganawa da Alƙalan bakwai tun ƙarfe 11 na safe, inda bai kammala ba sai 5:30 na yamma.

An fara taron dai inda Tanko Muhammad ya fara ganawa da su ɗaya-bayan-ɗaya, kamar haka: Daga na FCT Abuja sai Jihar Ribas, sai Kebbi, sai Kuros Riba, sai Jigawa, sai Anambra, sai na Jihar Imo.

Kowane Alƙalin dai Babban Jojin Najeriya ya titsiye shi ya na sheƙa masa ruwan tambayoyi har tsawon awa ɗaya. Daga baya kuma ya yi masu kuɗin-goro, ya tattara su wuri ɗaya, ya karanto masu kakkausan gargaɗi.

Tanko ya bada misali mai kaushi sosai ga waɗansu Alƙalai uku, inda ya ce masu, “daga yau kada ku kuskura ku sake irin wannan ɓamɓarma.”

Tanko ya ce Alƙalan uku waɗanda su ka yanke hukunci a cikin hukuncin wata kotu, za su bayyana a gaban Hukumar Ladaftar da Alƙalai domin fuskantar ladaftarwa.

An dai ga Babban Jojin Najeriya Tanko a cikin fushi ya na cewa idan aka yi wa shari’a ɗaya dameji, to tamkar an yi wa dukkan shari’u ne baki ɗaya.

“Saboda haka tilas ku daina kasassaɓa da ɓamɓarmar bayar da hukunci a cikin wata shari’ar da wata kotu ta yanke hukunci. Domin wannan tamkar kwance wa shari’a zane a kasuwa ku ke yi.”

“A matsayin ku na Shugabannin Kotu, ayyukan ku su na da kima sosai. Daga yau ku daina wannan sakarcin da ku ke yi, musamman tsoma dungulmin ku cikin dagwalon siyasa.”

Share.

game da Author