Babban Jojin Najeriya ya ce a ladabtar da jojin Abuja, wanda ya aika wa Charles Soludo sammacin jangwangwama

0

Babban Jojin Najeriya Tanko Muhammad ya bada umarnin a ladabtar da Alƙalin Kotun Yanki na Abuja, saboda ya yi kasassaɓar aika wa tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya Charles Soludo sammaci na aikata laifin da bai aikata ba.

Soludo a yanzu haka shi ne ya ɗan takarar gwamnan Jihar Anambra a ƙarƙashin jam’iyyar APGA.

Alƙalin mai suna Gambo Garba wanda ke Kotu Upper Area Court ta Zuba, ya aika wa Soludo sammwcin cikin watan Yuli, saboda zargin bai bayyana yawan kadarorin sa a lokacin da ya ke Gwamnan CBN ba, tsakanin 29 Ga Mayu, 2004 zuwa 29 Mayu, 2009.

Wani mai suna Oliver Butrus ne ya shigar da ƙorafi a kotun a kan Soludo, cewa a lokacin da ya ke Gwamnan CBN, ya karya dokar CCB, tunda bai bayyana yawan kadarorin sa ba.

Ya ce har yau babu wanda ya san halastacciyar dukiyar da Soludo ya tara, tunda bai bayyana yawan kadarorin sa ba, kamar yadda dokar Najeriya ta gindiya.

Sammacin da Alƙali Gambo ya tura wa Soludo ya na nufin ya amince ya hukunta Soludo a bisa buƙatar Bitrus.

Mutane da dama sun yi tir da Alƙalin wanda ya yi katoɓarar aika wa Soludo da sammacin. Saboda kotun ta sa dai ta na sauraren batutuwa ne da su ka shafi shari’ar Musulunci.

Majiya daga sashen shari’a na Najeriya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa Babban Jojin Najeriya ya dugunzuma sosai kuma ya ji kunyar wannan abin kunya da Alƙali Gambo ya tafka.

“Babban Jojin Najeriya ya bada umarnin ga Hukumar Ladaftar da Alƙalai ta Ƙasa (NJC) ta Abuja ta gaggauta ɗaukar matakan ladabtarwa na gaggawa a kan Alƙalin ‘Upper Area Court’, wanda ya yi kasassaɓar aika wa Charles Soludo sammaci.”

“Ya yi kasassaɓar aika masa da sammacin tuhumar da kasawa ko ƙin bayyana kadarorin sa, a lokacin ya na Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), tsakanin Mayu 2004 zuwa 2009.

Share.

game da Author