Ba mahara sojojin Najeriya ke kashewa a Zamfara ba, mutanen da basu ji ba basu gani ba ake kashewa – In ji Gumi

0

Fitaccen malamin addini, mazaunin jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa maimakon kashe ‘yan bindiga sojojin Najeriya na kashe mutanen gari ne da basu ji ba ba su gani ba.

” Ranar Alhamis wasu suka zo gidana suka zo min da kukan cewa ‘yan bindiga sun sace musa ‘yan uwa. Dukkan su an dauke musu ‘yan uwane a garin Rigachikun da Keke. Sun ce wai maharan da aka fatattaka ne suka shiga daga nan suka dauke musu ‘yan uwa.

Gumi ya ce bai ga amfanin kashe ‘yan bindiga da ake yi ba. Maimakon haka kyale su ya kamata ayi a rika yi musu wa’azi da gyara musu tarbiyya.

” Yanzu yan bindigan duk sun gudu sun wasu zuwa wasu yankunan. Kuma hakan hadari ne ga Najeriya. Ni fa a gani na ‘yan siyasa da ke wawushe kudaden Najeriya sune ‘yan ta’adda fiye da wadannan da ake fafura ake kashe wa.

” An gwada fatattakar su ta tsiya amma ba a samu nasara ba sai ma taɓarɓarewar tsaro da aka samu. Yanzu idan aka ci gaba za su koma su nemi afkawa harkar ta’addanci kai tsaye, shike nan sai kuma a koma gidan jiya.

Ba tun yanzu ba Gumi yake kira da maimakon a darkake su, shi shawarar sa shine abi su ta lalama, a yi sulhu ne da su. Gwamnan Zamfara da Katsina sun rungumi wannan khuɗuba sai dai kuma bata amfanar da su da mutanen jihohin su ba domin karin azaba ne mutane suka dulmiya ciki daga ƴan bindiga, har dai suka janye daga wannan shawara ta malam.

Sace-sace yaran makaranta ya ƙaru, kashe-kashen mutanen da basu ji ba basu bani ya yawaita, gaba ɗaya komai ya dagule babu sauki.

Da yawa masu yin sharhi sun soki wannan shawara ta Sheikh Gumi cewa ba zai yiwu ana kashe mutane su kuma masu kidan kana bin su ka na lallaɓasu ba, sannan kuma ba ji suke yi ba. Hakan ma tunzura su yake yi.

Gwamnonin Kaduna da Neja sun turje cewa atitir ba za su zauna da ƴan bindiga ko su biya kudin fansar wanda suka sace ba.

Share.

game da Author