Ba da yawun mu sakataren Miyetti Allah na Kasa, ya kantara wa Masari kalaman ɓatanci ba – Miyetti Allah, reshen jihar Katsina

0

Kungiyar Miyetti Allah, reshen jihar Katsina ta nisanta kanta da kalaman batanci da sakataren kungiyar na Kasa Sale Alhassan yayi da ya kira Masari a ‘tantirin mashayi.

Sakataren kungiyar reshen jihar Katsina Hassan Kuraye ya shaida cewa ba da yawun su sakataren kungiyar Miyetti Allah ya yi wannan kalamai ba.

” Ko bayan ya yi kalaman mun kira shugabannin uwar kungiyar suma sun shaida mana cewa ba da yawun kungiya ya yi wannan magana ba.

Kungiyar ta aika da sakon bada hakuri ga gwamna sannan ta ce za ta kawo masa ziyara ta musamman tare da sauran shugabannin kungiyar ta Ƙasa domin a baiwa Masari hakuri.

Sakataren Kungiyar Miyetti Allah ta ƙasa Saleh Alhassan ya maida wa gwamnan Katsina Aminu Masari da martani ba sa cewa da yayi,Fulani ne akalla kashi 70 suke ayyukan hare-hare da kashe-kashe a faɗin kasar nan.

Masari ya faɗi haka ne a hira da yayi da talbijin ɗin Channels.

Sai da faɗin haka bai yi wa sakataren Kungiyar Miyetti Allah daɗi ba, sai ya maida masa da martanin cewa shima gwamnan ‘Ɗan maskewa ne’

Jigar Katsina kamar jihar Zamfara na fama da tsananin hare-haren ƴan bindiga a yankin Arewa Maso Yamma.

Sai dai kuma a cikin makonnin biyu da suka wuce sojojin Najeriya sun bi su har cikin ƙungurmin daji suna ragargazar su.

Share.

game da Author