AREWA A HANNUN ‘YAN BINDIGA : Badaru ya gargadi Miyetti Allah karsu baiwa batagari wajen zama a Jigawa

0

Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammad Badaru, a ranar Juma’a, ya gargadi ‘yan kungiyar Fulani na Miyetti Allah, dasu kar su baiwa batagarin matasan Fulani wajen zama a rugagensu duba da yawan sace-sacen jama’a domin neman kudin fansa a Jihar.

Gwamnan Badaru yace duk wadanda aka kama da laifin garkuwa da mutane a rugagen Fulani suke ajiye mutanen domin neman kudin fansa, saboda haka yace gwannati bazata bari Jigawa ta dawo Lamar Zamfara ba.

Ana zargin cewa wasu ‘yan bindaga dake gujewa luguden wutan sojoji a Zamfara suna kaura zuwa wasu jihohi dake makwabtaka da su. Jihar Jigawa tayi suna wajen zaman lafiya, amma lamura sun fara daukar sabon salo sakamakon yawan sace-sacen jama’a a fadin Jihar a ‘yan kwanakin nan.

” Kune shuwagabanin Fulani, ya kamata kuyi magana da Hardodi da Bulamai da Shuwagabanin Rugaje, aja kunnensu sun san masu barna, kuma sun bari ana yi, idan an sace mutane, rugage ake kaiwa.

” Bamu so mu tura Sojoji Rugage su farma jama’a, ku taimaka mana su daina bari ana wannan abu in anga alamun yara lalatattu sunzu ayi magana da wuri domin a dauki mataki.

” Kar a bata mana Jiha, yanzu abinda yake faruwa a Zamfara bai yi dadi ba, kar a bari Jigawa ta kai wannan matsayi irin na Zamfara, inji gwamna Badaru.

Gwamnan Badaru yace gwamnatin Jigawa zata ci gaba da baiwa harkar ilimi na ‘ya’yan Fulani muhimmanci (Nomadic school) ta hanyar gina makaruntun ‘ya’yan makiyaya da kuma daukar ‘ya’yan makiyayan a matsayin malamai.

Malam Habibu Kila, Mai Magana da yawun Gwamna Badaru yace dama can a akwai makaruntu sama da 400 na ‘ya’yan Fulani kuma gwamnati na sharin gina wasu sabobbi guda 200 a fadin Jihar domin inganta karatun ‘ya’yan makiyayan.

Gwamnatin kuma na shirin daukar malamai ‘ya’yan makiyaya harsu 270 domin koyarwa a makarantun, inji Habibu Kila.

Jami’in ya kuma cewa gwamna Badaru yaje kasar Netherlands domin bunkasa harkar kiwo na zamani a inda za’a samu irin ciyawa wanda zai ringa fitowa a kowane lokaci cikin rani da damuna domin shanu su samu abinci.

Share.

game da Author