Tsohon gwamnan jihar Barno, Ali Modu Sheriff ya bayyana cewa ɗaya daga cikin burin Jam’iyyar APC shine ta yi mulki a Najeriya har na tsawon shekaru 40 ba tare da an samu matsala ba.
Amma kuma kafin a iya cimma wannan buri dole sai an samu direba gawurtacce, tantiri sannan kaifi ɗaya wanda zai shugabanci jam’iyyar musamman a daidai lokacin da Buhari zai kammala zangon sa ta biyu ya sauka daga kujerar mulki.
Sanata Sheriff na daga cikin waɗanda suke muradin tsayawa takarar shugabancin jam’iyyar.
” Yanzu shekarar APC 6 kacal akan mulki, burin mu shine mu shekara 30 zuwa 40 muna mulki a Najeriya.
” Hakan ya sa naga ya dace in zazzagaya in gana da shugabannin jam’iyyar, matasa da mata in gaya musu cewa kowa ya zo a haɗa hannu domin mu kai ga nasara, mu kuma cimma burin mu na zama daram a kujerar mulki na tsawon shekaru 30, 40 kai harma zuwa 50.
Yin haka kuwa sai gogagge, tantiri wanda ya kware wurin haɗa kan mutane da tsawata.
Sheriff ya ce yayi wa APC tanadi da shiri mai tsawo wanda ba za a samu matsala ba idan an kai tsakiyar teku.
Sauran waɗanda ke cikin jerin masu neman ɗarewa kujerar shugabancin APC din sun haɗa da tsohon gwamnan Nasarawa Tanko Almakura, Kashim Shetima, Danjuma Goje, AbdulAziz Yari, Ibrahim Baba da Sunny Moniedafe daga jihar Adamawa.
Discussion about this post