ANA WATA GA WATA: ‘Yan bindiga sun ragargaza sansanin Sojoji a Zamfara, sun kashe jami’ai 12

0

Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa mahara sun dira sansanin sojojin dake Mutumji, Karamar hukumar Dansadau ranar asabar sun kashe sojoji da yan sanda.

Wannan harin yayi sanadiyyar rayukan sojojin sama 9, ‘yan sanda biyu da sojan kasa 1.

Bayan kashe jami’an tsaro da ‘yan bindiga suka yi, sun kwashe makaman sojojin da suka kashe sannan suka banka wa sansanin wuta gabadayan sa.

A cikin makon jiya, yan bindiga sun baro jirgin yaki dake musu aman luguden wuta daga sama. Sai dai kuma rundunar sojin sama ta sanar cewa direban jirgin bai ji rauni ba.

Share.

game da Author