Hukumar Daƙile Cututtuka Masu Bazuwa ta Ƙasa (NCDC), ta bayyana cewa zuwa ranar 2 Ga Satumba, 2021, ƙididdiga ta tabbatar da cewa cutar kwalara ta kashe mutum 2,141 kuma mutum 65,145 ne su ka kamu da cutar a cikin jihohi 23 da Gundumar FCT Abuja.
NCDC ta bayyana wannan ƙididdiga a shafin ta na yanar gizo ranar Litinin, wanda ta ke tattara ƙididdigar adadin waɗanda su ke kamuwa da cutar kwalara duk bayan mako ɗaya.
Rahoton dai ya nuna mutum 855 ne su ka kamu da kwalara a mako na 34 a Jihar Bauchi. Sai mutum 396 a Jihar Katsina, wasu 306 a Jihar Kano waɗanda su ka tashi zuwa kashi 73.2% kenan na mutum 2,127 da su ka kamu a mako na 34.
Sauran jihohi sun haɗa da Yobe (162), Zamfara (80), Neja (78), Barno (67), Sokoto (45), Kaduna (41), Gombe (21), FCT (18), Kebbi(17), Adamawa (15), Taraba (13), Nassarawa (10), Filato (2) sai kuma Jigawa (1).
NCDC ta ce ƙididdiga ta kama ne tun daga farkon 2021, kuma kwalara ɗin ta kama tun daga ɗan shekara 5 zuwa masu shekaru 14, waɗanda su ne ta fi kamawa da su ka haɗa da yara maza da mata.
Jimillar adadin waɗanda su ka kamu da cutar sun kasu kashi 51 na maza sai kashi 49 mata.
“Jihohi 23 da FCT Abuja ne su ka bada rahoton ɓullar cutar kwalara a cikin wannan shekara ta 2021. Sun haɗa da Benuwai, Delta, Zamfara, Gombe, Bayelsa, Kogi, Sokoto Bauchi, Kano, Kaduna, Filato, Kebbi, Kuros Riba, Nasarawa, Neja, Jigawa, Yobe, Kwara, Adamawa, Enugu, Katsina, Barno, Taraba da FCT Abuja.”
Watanni biyu da su ka gabata PREMIUM TIMES Hausa ta buga dalilan da su ka sa kwalara ke fantsama a cikin al’umma.
Matsalolin Da Su Ka Haifar Da Fantsamar Cutar Kwalara A Jihohi 22 Da FCT Abuja.
Hukumar Hana Bazuwar Cututtuka ta Ƙasa (NCDC) ta bayyana cewa zuwa ranar 1 Ga Agusta, 2021, mutum 31,425 su ka kamu da cutar amai da gudawa, ko kuma kwalara, yayin da cutar ta kashe mutum 1000 a cikin wannan shekara.
Sai dai kuma binciken da PREMIUM TIMES ta gudanar a wasu garuruwa da ƙauyuka da lungunan cikin jihohi 22, ya nuna lamarin ya yi munin da ya wuce hasashen da Gwamnatin Tarayya ta bayyana, nesa ba kusa ba.
PREMIUM TIMES Hausa ta bi diddigin rahotannin, ta tsakuro wasu dalilan da ke haddasa ɓarkewar amai da gudawa a cikin al’umma, musamman inda babu ingantattun ababen rayuwa.
Cikin jihohin da PREMIUM TIMES ta bi diddigi sun haɗa da Kano, Jigawa, Katsina, Zamfara, Sokoto, Kebbi, Benuwai, Filato, Ebonyi da Enugu.
1. Rashin tsafta da barin ƙazanta a gida, musamman abinci da kayan abinci ko kwanukan cin abinci.
2. Zubar da tulin shara da bola aikin unguwanni, wadda ruwan sama ke maida ƙazantar ta s cikin jama’a.
3. Zubar da shara ko bola ko bayan gida a cikin ƙaramu da magudanan ruwa.
4. Yin bayan gida a fili ko a kan bola.
5. Rashin ruwa mai tsafta a cikin al’umma.
6. Ƙarancin asibitocin kula da marasa lafiya a cikin jama’a marasa galihu.
7. Ƙaranci ko rashin magungunan da za a bai wa mai cutar kwalara cikin gaggawa.
8. Matsalar ƙarancin jami’an kiwon lafiya a cikin jama’a.
9. Rashin hanyoyi masu kyau da za a garzaya asibiti da mai cutar amai da gudawa cikin gaggawa.
10. Shan ruwan ƙarama ko kogi, wanda ake zubar da shara, kashin dabbobi da kuma bayan gida.
Discussion about this post