Al’ummar Arewa maso Yamma sun yi murna da toshe wayoyin tarho, sun ce ba su damu da takurar rashin waya ba

0

Al’ummar jihohin Kebbi, Sokoto da Katsina sun bayyana cewa a shirye su ke su jure duk wata takura da ƙunci da matsin da za su shiga sakamakon kulle lambobin wayoyin sadarwa da aka yi a Jihar Zamfara, matsawar dai yin hakan zai kakkaɓe masu ‘yan bindiga a yankunan su.

Sun ce takurawar da su ke fuskanta da zaman ƙunci dama tilas ya faru idan aka kai ga kulle layukan wstoyini, amma har gara su fuskanci wannan ƙuncin idan dai za a kawar da ‘yan bindiga sanadiyyar ɗaukar tsatstsauran matakin.

Da yawa ma daga cikin su su na nuna haushi ganin yadda wasu ke ƙorafe-ƙorafe da kuma nuna damuwar su a kan kulle layukan wayoyin da Gwamnatin Tarayya ta yi a yankunan na su.

Sun ce bai kamata a riƙa ƙorafi ba, domin matakin dai an ɗauke shi ne don a kare rayukan al’ummar yankin.

Sun ce dama an ce ‘magani ɗaci gare shi, amma kuma warakar da ya ke samarwa ta fi ɗacin daɗi nesa ba kusa ba.

“Ni dai na tabbatar cewa wannan halin ƙuncin da aka shiga na rashin sukunin kiran lambobin waya, mai wucewa ne.

“To irin mawuyacin halin da mu ke ciki, idan ma an bar ka da wayar, amfanin me za ta yi maka? Tun ‘yan bindiga su kassara mana harkokin kasuwanci da sauran mu’amalolin rayuwa.”

Garin Bena ɗaya ne daga cikin garuruwan Jihar Kebbi, amma kuma ya yi iyaka da Jihar Zamfara. Kulle wayoyin tarho da Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NCC) ta yi a ranar 3 Ga Satumba a Zamfara, ya shafi wasu sassa na Bena.

Mutanen garin sun bayyana cewa duk da katse wayoyi da aka yi, kuma harkokin tattalin arzikin su ya girgiza, to su dai sun yi murna da ɗaukar wannan ƙwaƙƙwaran mataki da aka yi.

Mazauna garin da dama sun bayyana irin mawuyacin halin da su ka shiga sakamakon hare-haren da ‘yan bindiga ke kaiwa.

Babangida Sa’adu, Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Malamai ta Jihar Sokoto, ya roƙi Gwamnanti a faɗaɗa dokar kulle wayoyi ba a jihar Zamfara kaɗai ba, har dukkan sauran jihohin da ke maƙautaka da ita.

“Saboda mu na jin labarin cewa wannan mataki da aka ɗauka ya na yin tasiri sosai. Saboda Sojojin Najeriya su na isa har inda ‘yan bindiga su ke, su na ragargazar su. Saboda babu masu kiran ‘yan bindiga a waya su na yi masu kwarmaton abin da jami’an tsaro ke ciki.”

Share.

game da Author