Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa nan ba da daɗewa ba za ta fara daukar mataki game da waɗanda suke kin yin rigakafin korona a ƙasar nan.
A ranar Talatar makon jiya ne shugaban hukumar kula cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko ta ƙasa NPHCDA Faisal Shu’aib ya sanar da haka a taron manema labarai a Abuja.
Shuaib ya ce gwamnati za ta yi “amfani da tsarin doka” wajen tilasta wa mutanen da suka ki yin allurar rigakafin saboda kada yaɗuwar cutar ta yaɗu gadan-gadan kamar yadda ya ke.
Haka shima a ranar Alhamis ɗin makon jiya sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya bayyana cewa gwamnati za ta tilasta yin allurar rigakafin cutar korona ga duk ma’aikatan gwamnatin tarayya.
Mustafa ya ce yin haka ya zama dole ganin yadda ma’aikatan ke gudanar da aiyukka a ciki da wajen kasar nan a madadin gwamnati.
Mustafa ya ce gwamnati za ta fara tilasta wa ma’aikatan yin allurar rigakafin korona da zaran kasan ta samu isassun allurar rigakafin cutar domin kowa da kowa.
Zuwa yanzu gwamnati ta yi wa mutum sama da miliyan uku allurar rigakafin korona inda daga ciki kisan mutum miliyan biyu sun yi allurar rigakafin zango na biyu.
Idan ba a manta ba a wannan mako ne
Babbar Kotun Fatakwal da ke Jihar Ribas ta dakatar da Gwamna Godwin Obaseki na Jihar Edo daga ƙaƙaba dokar hana shiga masallatai da coci-coci sai da katin shaidar rigakafin Korona.
Obaseki ya saka dokar hana mutane shiga masallatun, coci-coci, manyan kantuna da sauran wuraren da mutane ke taruwa idan ba sun nuna katin shaidar yin allurar rigakafin korona ba.
Kafin gwamnati ta fara yi wa mutane allurar rigakafin gwamnati ta shaida wa mutane cewa ba za ta tilasta mutane yin allurar rigakafin korona ba amma za ta wayar da kan mutane kan mahimmancin yin allurar rigakafi.
Zuwa yanzu gwamnati ta yi wa kusan mutum miliyan hudu allurar rigakafin korona inda daga ciki mutum sama da miliyan biyu sun yi allurar rigakafin korona zango na biyu.
Mutum 444 sun kama cutar korona bakwai sun mutu a Najeriya ranar Juma’a.
Hukumar NCDC ta bayyana cewa an samu karin mutum 444 da suka kamu mutum 7 sun mutu a dalilin kamuwa da cutar korona ranar Juma’a a Najeriya.
Hukumar ta ce an gano wadannan mutane a jihohi 20 da Abuja.
A jimla mutum 194, 088 sun kamu mutum 2,495 sun mutu.
An sallami mutum 179,679 sannan mutum 11,914 na dauke da cutar
Sannan a ranar Laraba mutum 11 ne suka mutu, mutum 582 sun kamu a kasar nan daga jihohi 15 da Abuja.
Yaduwar cutar
Legas – 73,265, Abuja-20,666, Rivers-10,701, Kaduna-9,258, Filato-9,205, Oyo-8,298, Edo-5,596, Ogun-5,293, Kano-4,089, Akwa-ibom-4,077, Ondo-3,968, Kwara-3,562, Delta-3,003, Osun-2,725, Enugu-2,563, Nasarawa-2,415, Gombe-2,258, Katsina-2,212, Ebonyi-2,048, Anambra-2,108, Abia-1,820, Imo-1,721, Bauchi-1,567, Ekiti-1,504, Benue-1,438, Barno-1,344, Adamawa-1,136, Taraba-1,062, Bayelsa-1,567, Niger-968, Sokoto-796, Jigawa-568, Yobe-501, Cross-Rivers-483, Kebbi-458, Zamfara-253, da Kogi-5.