Ranar 2 ga watan Maris 2021 Najeriya ta zama kasa ta uku a cikin jerin kasashen da suka karbi allurai miliyan hudu na Oxford/ AstraZenece a yankin yammacin Afirka, bayan kasashen Ghana da Ivory Coast, ta hannun COVAX ko kuma gidauniyar kasa da kasa ta samar da allurar rigakafin COVID-19.
Kawo yanzu gwamnatin Najeriya ta ce ta yi amfani da milliyan 3.97 na AstraZeneca a yayinda mutane miliyan 1.42 kuma sun karbi allurar a kasar baki daya.
Ba da dadewa ba gwamnatin Najeriya ta sake samun wasu alluran miliyan hudu na Moderna a matsayin gudunmawa daga Amurka, don taya kasar yaki da zagaye na uku na barkewar cutar. Hukumar UNICEF ce ta karbi wadannan allurai a madadin Najeriya. Alluran sun sauka a Abuja tashar jirgin saman Nnamdi Azikiwe a jirage biyu.
Bayan nan, kasar ta sake samun wasu karin 177,600 na Johnson & Johnson, shi kuma ta hannun kungiyar Tarayyar Afirka wato AU a ranar 12 ga watan Agusta 2021.
Hukumar NPHCDA, wadda ke tabbatar da cigaban kiwon lafiya a matakin farko na al’umma ta ce wannan adadin, rukunin farko ne da kungiyar ta AU kuma za’a cigaba da karbar magungunan kowane wata har sai an sami miliyan 29.8 wanda shi ne cikakken adadin da aka alkawarta mata.
Cikakken bayani kan kowace allura
Allurar Oxford-AstraZeneca kwayar cutar ce da aka kirkiro a jami’ar Oxford tare da taimakon kamfanin magunguna na AstraZeneca ke cikin allurar da ake bayarwa. A cewar Medical News Today, jaridar da ke bincike da rubutun batutuwan da suka shafi kiwon lafiya, ta ce wannan kwayar cutar na dauke da wasu kwayoyin halitta da ke kwaikwayon nau’in abincin da ake kira furotin ko protein a turance, wanda aka saba gani a saman kwayar cutar SARS-CoV-2. Da zarar ta shiga jikin mutun, kwayoyin halittan kan sanya wasu kwayoyin jikin su fara sarrafa protein. Kasancewar wannan nau’i na protein ne ke taimakawa jiki ya fara sarrafa kwayoyin da za su inganta garkuwan jikin mutun wajen yakar cutar COVID-19 ko da ya shiga jikin. Allurar ta na da wa’adin watanni shidda ne kadai idan aka sa fridge mai sanyin digiri 2 zuwa 8 bisa ma’aunin Selshiyus. Idan har aka cire daga cikin fridge ana iya ajiye ta a wurin da ke da sanyin digiri 2 zuwa 25 a ma’aunin selshiyus na tsawon sa’o’i shidda ne kadai.
Allurar Moderna an yi mata lakabi da suna mRNA-1273 kuma kamfanin Moderna ya sarrafa, tare da Cibiyar kasa ta nazarin rashin lafiya da cututtuka masu saurin yaduwa na Amurka (NIAID) da hukumar bincike da tattabar da ci-gaban illimin halitta (BARDA). Allurar rigakafin Moderna allurar da aka fi sani da mRNA ce wato kwayar halittar da ake sarrafawa, wadda ke baiwa jikin umurnin sarrafa sinadarin da ake kira spike protein ya kuma koya wa jikin yadda zai iya gane shi. Da zarar aka yi haka garkuwan jikin mutun zai fara yakar spike protein a duk sadda ya gan shi. A cewar kamfain allurar tana da karfin yakar cutar da kashi 90 cikin 100 kuma a lokutan da cutar ta ke da tsanani, karfin yakar na iya kaiwa har kashi 95 cikin 100, idan aka kara yin allurar watanni shidda bayan da aka karbi kashi na biyu.
Johnson & Johnson ce allura ta uku wadda Hukumar kula da abinci da magunguna na Amirka ta amince a yi amfani da ita a mataki na gaggawa wajen magance cutar a jikin mutun, bayan Pfizer da Moderna. Ko da shi ya banbanta kadan daga Pfizer da Moderna, domin Johnson & Johnson ya fi kama da Oxford-AstraZeneca tunda su sun yi amfani da kwayar cutar ne mara lahani wajen aikar da irin umurnin da jiki ke bukata dan gini garkuwar jiki.
Banbancin Oxford-AstraZeneca, Moderna da Johnson & Johnson
Banbancin da ke tsakanin Moderna, da Johnson and Johnson da AstraZeneca ba yawa, kuma su ne allurai ukun da aka kawo Najeriya. Duk ukun kuma Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta amince a yi amfani da su a lokacin da ake bukata da gaggawa, ita ma hukumar NAFDAC ta amince da hakan.
Oxford-AstraZeneca ce allura ta farko da aka fara amfani da ita a Najeriya kuma bisa bayanan wani rahoton BBC, an sarrafa shi ne da kwayar cutar mura (wadda ake kira adenovirus) wadda aka samu daga biri amma an inganta shi da kwayoyin halittan da ke dauke a coronavirus – sai dai ba zai iya janyo ciwo ba.
Allurar Moderna wanda gwamnatin Najeriya ke amfani da shi yanzu ana iya ajiye shi a fridge mai sanyin digiri 2 zuwa 8 a ma’aunin selshiyus, kuma alluran da ba’a bude ba suna iya zama cikin fridge na tsawon kwanaki 30 a cewar hukumar yaki da cututtuka CDC. Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta shawarci ba da tazarar kwanaki 28 tsakanin alluran biyu. Allurar na da karfin bayar da kariya na kusan kashi 94.1 bisa 100 daga kwanaki 14 bayan karban kashin farko na alluran.
Johnson & Johnson na bukatar sanyi sosai a wurin ajiya. A cewar kamfanin, allurar na iya kaiwa har shekaru biyu idan har aka ajiye ta a dakin sanyi mai digiri -20 (ashirin kasa da sifili) bisa ma’aunin selshiyus sa’annan shi ma zai iya kai wa kwanaki 30 a cikin fridge mai sanyin digiri 2 zuwa 8 a ma’aunin selshiyus.
Da yake bayani kan allurar, babban darektan NPHCDA Dr Faisal Shu’aib ya ce J & J ba ya bukatan wani sanyi na musamman ana iya ajiye shi kamar yadda ake ajiye sauran alluran rigakafi. Haka nan kuma, inda Johnson and Johnson ta fi Moderna da Oxford-AstraZeneca shi ne allura daya ake bukata ba biyu ba kamar sauran. Dan haka ya fi su saukin hulda tunda zai rage wahalar zuwa wurare masu nisa da wahalar shiga.
Dr Shu’aib ya ce za’a yi amfani da kashin farko na alluran J&J a yankunan da ke da wahalar shiga da kuma tsofaffi wadanda ba su da karfi sosai, a duk fadin kasar tun da sau daya kadai ake yi.
Abin da Kwararru a Najeriya ke ce wa
A yayin da ake cigaba da samun karuwar masu fargaba dangane da banbancin alluran rigakafin COVID-19 da ke shigowa kasar, kwararru a Najeriya sun kwantar da hankulan jama’a kan alluran uku, inda suka ce NAFDAC ta amince a yi amfani da dukansu uku har ma ta ce za’a iya amfani da su a kan wadanda suka kamu da cutar a matsayi na gaggawa kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bayyana.
Hukumar kula da lafiya ta kasa NPHCDA da kungiyar likitocin Najeriya (NMA) sun jaddada cewa Moderna, Johnson & Johnson da Oxford-Astrazeneca duk amintattun allurai ne wadanda ke da karfin yaki da COVID-19.
Babban darektan NPHCDA Faisal Shu’aib yayin da ya ke zantawa da manema labarai a Abuja ya sake tabatarwa ‘yan Najeriya cewa duk wata allurar da NAFDAC ta aimince da ita, na da karfin byar da kariya da kuma yakar cutar.
NPHCDA ta ce duk wadanda suka riga suka karbi kashin farko na allurar AstraZeneca za su karbi na biyun a watan Ogosta sadda raguwar 5000 din da ake sa ran samu za su iso kasar. Da cewa haka, Dr Shu’aib na nufin cewa bisa shawarar WHO bai kamata wanda ya karbi AstraZeneca ya ji ya anshi Moderna da aka kawo yanzu ba, wajibi ne ya karasa da AstraZenecar da ya riga ya fara.
Ita ma kungiyar likitocin Najeriya (NMA) ta sake kwantar da hankulan jama’a dangane da allurar Moderna, inda ta ce lallai allurar na da karfin yakar kwayar cutar COVID-19. Shugaban kungiyar Dr Japhet Olugbodi ya ce “Moderna na da karfin kashi 94 cikin 100 na kare jama daga kamuwa da cutar sa’annan kashi 90 cikin 100 na kumawa da matsanancin nau’in cutar.
Discussion about this post