A BUDE KUNNUWA A SAURARE NI: Sauke Nanono da Saleh ba shine karshen sauye-sauye da za a gani ba – In ji Buhari

0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa sauke ministan Noma, Sabo Nanono da yayi da na wutar Lantarki, Mamman Saleh, ba shine karshen sauye-sauye da za agani ba.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sauke ministocin ayyukan gona da na wutar Lantarki a ranar Laraba.

A wata sanarwa da Femi Adesina yan fitar da yammacin Laraba, shugaba Buhari ya maye gurbin su da ministocin Muhalli da na ayyuka da gidaje.

Ministan Muhalli, Mohammed Mahmood zai maye gurbin Sabo Na nono, sai kuma Abubakar Aliyu zai maye gurbin Mamman Saleh a ma’aikatar wutar Lantarki.

Buhari ya ce nan ba da dadewa za a aika da sunayen sabbin mutanen da za su maye gurbin wadanda aka sauya wa wurare.

Share.

game da Author