2023: Gwamna Bala na cin taliyar sa ta karshe ne a jihar Bauchi

0

Dan majalisan dake wakiltar Bauchi a majalisar Tarayya, ya hori magoya bayan jam’iyyar APC da su ci gaba yin biyayya da da’a ga jam’iyyar sannan su ci gaba da hakuri cewa saura kwanaki kadan Jam’iyyar ta tawo gida wato ta dawo APC.

Honarabul Yakubu Shehu ya ce dama dai akasi ne aka samu a 2019 har PDP ta yi nasara a zaben gwamna a Jihar, amma yanzu an like duk inda ya ke yoyo.

Jihar Bauchi ta APC ce, akasi aka samu har PDP ta yi nasara a zaben gwamna. Amma ina tabbatar muku cewa, taliyar karshe suke ci a gidan gwamnati, 2023, Bauchi za ta koma APC.

Idan ba a manta ba, jam’iyyar PDP ta kada APC a zaben gwamna da aka ya 2019. Wannan kayi da ta yi wa APC ya yi matukar kawo wa jam’iyyar cikas da koma baya a jihar Bauchi.

Share.

game da Author