2023: Dalilan da ya sa Atiku ne ya fi dacewa da cancantar zama ɗan takarar shugaban kasa a PDP, Daga Paschal Oluchukwu

0

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma wanda yayi wa jam’iyyar PDP takara Alhaji Atiku Abubakar shine mutumin yafi kowa gogewa da sanin halin da siyasar Najeriya take ciki.

Wannan ba bakon abu bane, wannan yasa na tsunduma da bincike don duba wasu batutuwa akan halin da Najeriya da jamiyyarmu take ciki yanzu.

A matsayina na mai nazari da kuma bibiyar halin da jamiyyar PDP take ciki, yanzu kan halin da jamiyyar take ciki tana bukatar kwararre wanda zai hadakan jigigon jamiyyar waje daya domin kareta daga rushewa ko yagewa.

Babu wani abu boyayye akan halin da ake ciki yanzu na kace – kace, da maida martani tsakanin juna, da kuma rigingimu a cikin jamiyyar tun daga shugabancin kasa, shiyya da kuma jahohi ga rigingimu tsakanin jigagan jamiyyar wanda kowa yake kokarin ganin ya kafa yaransa a shugabancin jamiyyar maimakon kashe wutar rikicin da ake ciki.

Duk da haka, daga wani bincike da masana sukayi, wannan halin da babbar jamiyyar adawa ta PDP take ciki ba bakon abu bane a siyasa ko rayuwa ba inda kowa yake kokarin kare bukatarsa. Shiyasa masanin siyasa dan kasa Jamus Ralph Dahrendorf yace rigima wajen kare bukata bakomai bace indai bukatar zata cimmu, wannan bakomai bane daga karshe dai dole dayane zaiyi nasara.

Yace, irin wannan rigima kanyin nasara wajen tabbatuwar cigaba mai dorewa ko samun fahimta tsakanin mutane masu banbancin ra’ayi, ba tare dasu din sun hade kansuba, ba tare da wani alkawariba sai kawai saboda tsawatarwar da wasu zasuyi .idan kuka duba yadda aka fara yunkurin cire shugaban jamiyyar na kasa, Prince Uche Secondus wanda baifi wata uku ya rage masa ya gama wa’adinsaba da kuma wasu rigingimu da suka dabai baye jamiyyar da har wasu suke canza shek’a zuwa jamiyya mai mulki, PDP zata iya shiga wani mugun hali indai ba’a samu wani kwararre wanda ake girmamawa kamar Atiku Abubakar ya shiga tsakani ba.

Zan kawo dalilan da sukasa dole Atiku ne yafi kowa cancanta a kasa.

Na farko, Atiku shine wanda ya fito yana ta kiraye kirayen a tabbatar da hadin kai kamar yadda yace, “PDP tafi karfin bukatar wani mutum tasa ta kansa. Ya kamata mu hada kanmu mu sanya jamiyya a gaba mu ajiye bukatarmu. Mubi a hankali kada mu mika kanmu hannun jam’iyya mai mulki.

“Baza mu amince da tsarin jamiyya daya ba a Najeriya wanda zai hana yan Najeriya damar canza gwabnati a 2023 ba” Abubakar yayi wannan kiran ta hannun mai taimaka masa akan kafafen yada labarai, Paul Ibe ranar 5 ga Ogusta na wannan shekarar.

Na biyu, Atiku bai dade da yin wani yunkuri na tabbatar da hadin kai tsakaninsa da gwabnan jihar Ribas, Nyesom Wike – wani jigo a cikin PDP wanda suka samu matsala akan wata bukatar sa a zaben fidda gwani na jamiyyar na 2019.

Yayin zaman wanda ya gudana a tsakaninsu, Atiku yace yan Najeriya suna jiran PDP tazo ta karbe ragamar mulki tun daga sama a 2023.

A matsayinsa na mai faɗin gaskiya, Atiku a matsayinsa na marar nuku nuku bai boye ba ya bayyanawa yan jarida cewa matsalolin jamiyyane suka kawosa Fatakwal domin samun daidaito tsakaninsa da gwabna Wike. Tabbas ya damu da samar da hadin kai, zaman lafiya a cikin PDP, wanda yace sune babban tsanin dazai tabbatar da nasarar mu a zabe 2023 shine hadin kai.

Na uku, Atiku yana da kwarewa akan tattalin arziki da samar da hanyoyin samar da ayyukanyi a daidai wannan lokacin da tattalin arzikin Najeriya yake wani mugun hali a karkashin wannan gwabnatin wanda sun kasa kawo wasu dabaru da zasu bunkasa tattalin arziki .a 2023, Najeriya tana bukatar mutumin da yake da kwarewa wajen tattalin arziki bawanda zai kara jefa mana tattalin arzikinmu cikin mugun haliba.

Yana da kyakkyawar dama duba da yankin da za’a tsaida dan takara, idan PDP ta tsaida dan takararta daga arewa 2023, Atiku wanda ya fito daga arewa maso gabas shine wanda yafi kowa gogewa a cikin jamiyyar dazai iya gogawa da jamiyya mai mulki ta kowanne fanni, musamman duba da yadda yan Najeriya da dama suka fidda tsammani da APC duba da yadda suka kasa cika alkawarin da suka dauka. Shine wanda ya ganawa fadar shugaban kasa azaba a zaben 2019 da ya gabata.

Yanzu shine wanda yafi kowa cancanta ya dawo da PDP kan mulki a 2023 musamman idan shuwagabannin jamiyyar sun hadiye maitarsu Sun maida hankalin su wajen dawowa kan madafun iko a Najeriya.

Duk da halin da Najeriya take ciki, Atiku yana cigaba da gudanar da kasuwancinsa cikin kwanciyar hankali. Wannan yasa gaba daya ya maida hankalinsa wajen hanyoyin da za’a samar da ayyukanyi ga matasa a 2019 yayin kamfen dinsa.

Atiku ya nuna damuwarsa akan yadda matasa mata da maza suke cikin wani irin yanayi na rashin aikinyi inda a lokacin 33% da 77% nasu basu da aiki kuma basu da ilimi kuma basu da dabaru. Idan ana bukatar magance matsalar, Atiku ne zai iya samarwa da matasa aikinyi da kuma tabbatar da an rage masu zaman banza da rage ta’addanci wanda duka talaucine yake kawowa.

Abun bakin ciki a Najeriyar mu ta yau, mafi akasarin wadannan matasan sun koma yan ta’adda, yan bindiga, masu garkuwa da sauran masu tada zaune tsaye, da kawo matsalar tsaro da kuma takurawa mutanenmu. Wannan shine babban abun da ya addabemu saboda yadda gwabnati ta gaza samar da ayyukanyi da a kalla matasa miliyan uku zasu samu aikinyi da kuma bawa yan kasuwa dama domin su samar da ayyukanyi kowacce shekara.

Abune sananne duk yan siyasar Najeriya a yanzu babu wanda yasan yadda zai hada kan kabilu, addinai da al’adun Najeriya waje guda kamar sa.

Atiku ya damu da halin da ake ciki, yana da kwarewa da kishin bunkasa tattalin arziki da samar da cigaba.

Tabbas, Idan tsohon mataimakin shugaban kasar ya samu dama zaku tabbtar da magana ta!

Share.

game da Author