Rundunar Ƴan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da harin da ƴan bindiga suka kai garin Shinkafi ranar Friday.
Sai dai kuma rundunar ta ce kafin su aikata ta’addanci su, jami’an ƴan sanda da Sojoji suka diran musu, suka fatattake su bayan sun jijji musu rauni.
Muhammad Shehu, kakakin rundunar ya karyata rahoton Daily Trust da suka ruwaito wai ƴan bindiga sun afka ofishin ƴan sanda a Shinkafi.
Shehu ya ce jami’an tsaro sun ci kwalar ƴan bindigan sun ji musu munanan rauni sannan suka fatattake su. Kuma babu jami’an tsaron da aka kashe ko kuma aka ji wa rauni. Sannan babu wani ɗan gari.
Rundunar ƴan sanda ba su ji daɗin yadda Daily Trust ta buga labari ba tare da tantance sahihancin sa ba. Muna kira ga ƴan jarida da su riƙa tantance labarai kafin su wallafa domin abinda ya shafi harkar tsaro na da matukar mahimmanci a tantance shi kafin a wallafa.