Ƴan sanda sun damke wasu abokai ƴan kungiyar matsafa dake tsafi da kawunan mutane a Ilori

0

A ranar Litinin ne kotun majistare dake Ilorin jihar Kwara ta daure wasu abokai maza biyar bayan kamasu da laifin kashe wa karuwa a karamar hukumar Pategi sannan da yin amfani da sassan jikinta wajen yin tsafi da shi.

Kotu ta kama Samuel Tsado, Mohammed Gbara, Mohammed Abubakar, Mohammed Ahmadu da Bala Katun da laifin haɗa baki, da yin kasuwancin sassan jikin wata karuwa da suka sace.

Alkalin kotun Wahab Saka ya yanke hukuncin daure wadannan mutane a kurkuku har sai bayan kotu ta kammala shari’ar.

Saka ya ce za a ci gaba da shari’a ranar 30 ga Satumba.

Lauyan da ya shigar da karar Isaac Yakub ya bayyana cewa a ranar 29 ga Yuli Tsado ya je ya dauko karuwar mai suna Abigail Polumuga daga Otel din ‘Victory Hotel’ inda tun daga lokacin ba a sake ganin ta ba.

“Tsado ya bayyana wa jami’an tsaro cewa da shi da abokansa suka fille mata kai da sharɓebiyar takobi sannan suka yi amfani da sassan jikinta wajen yin tsafi.

Yakub ya ce kama Tsado da rundunar ƴan sanda suka yi ya taimaka wajen kamo abokan sa hudu sannan kuma rundunar ta ci gaba da farautar sauran mutum biyu dake da hannu a shirya kisan karuwan.

Ya roki kotun da ta daure wadannan mutane har sai an kammala shari’a.

Share.

game da Author