Zanga-zanga ta ɓarke sanadiyyar karyewar darajar Bitcoin na kasuwancin hada-hadar cryptocurrency.
Karyewar darajar ta faru ne bayan da ƙasar El Salvador ta bayyana cewa ta amince ƙasar ta yi amfani da Bitcoin a matsayin kuɗaɗen hada-hadar ƙasar.
Ranar Laraba ɗin nan ce Bitcoin ya karye a kasuwa, bayan da kafin nan sai da ya kai darajar dala 64,000 a cikin watan Afrilu. A cikin Agusta kuma ya koma dala 50,000.
Masu zanga-zanga dai sun zargi ƙasar El Salvador da yin akarambanar da ya haddasa karyewar darajar Bitcoin ɗin.
Shugaban El Salvador Nayib Bukele dai tun a ranar Litinin ya bayyana sayen dala miliyan 21 ta cyrptocurrency.
Tun cikin watan Yuni ne shugaban El Salvador ya miƙa ƙudirin neman amincewar Majalisar ƙasar, cewa su amince a faɗin ƙasar a riƙa amfani da Bitcoin.
Nan da nan ‘yan majalisa 62 su ka amince daga cikin mambobin 84 su ka rattaba amincewa.
Bayan rattaba hannun dai farashin Bitcoin ya koma dala 34,239.17.
Sai dai kusan kashi 68 bisa 100 na waɗanda aka tattauna da su, sun ƙi yarda a riƙa amfani da Bitcoin a ƙasar a dukkan hada-hadar kuɗaɗe, ko wace iri ce.
Yanzu dai farashin ya faɗi warwas daga dala 52,000 zuwa dala 43,000.
Cikin watan Agusta ne dai Darajar ‘Bitcoin’ ta haura dala 50,000 bayan karyewar da ƙwandalar ta yi cikin watan Afrilu.
A wancan lokacin sai da darajar ƙwandalar hada-hadar ƙuɗaɗe ta ‘Bitcoin’ ta sake tashi zuwa sama da dala 50,000 a duniya, a ranar Litinin, bayan karyewar martabar kuɗin, watanni uku da su ka gabata.
Ƙwandalar a ranar Litinin wajen ƙarfe 2:20 na yamma ta kai dala 50,274.68 daidai agogon Najeriya.
Hakan ya faru ne a daidai lokacin da ake raɗe-raɗin cewa Amirkawa za su ƙara narka kuɗaɗe hada-hada, ta yadda za a ƙara samun riba.
‘Bitcoin’ ya ƙara daraja da kashi 2.84 cikin sa’o’i 24. Wato kashi 6.25 kenan a kowane mako.
Yayin da ƙarfin jarin ‘Bitcoin’ a kasuwannin hada-hada a yanzu ya kai dala biliyan 31,449,905,210.17. Wato ya ƙaru kenan da kashi 8.49 bisa adadin sa na baya.
Cikin watan Afrilu ne dai darajar hada-hadar amfani da ‘Bitcoin’ ta yi ƙasa warwas, inda a ranar 14 Ga Afrilu ya yi ƙasa, bayan ya kai dala 64,863.10.
Shi ma farashin cyrptocurrency na Ether ya tashi da kashi 2.8, wato ya kai dala 3,337.
Hakan na nufin ya tashi da kashi 91 bisa 100, bayan ya yi ƙasa zuwa dala 1,740 a cikin watan da ya gabata.
Kafofin yaɗa labarai a Turai sun bayyana cewa ƙwandalar cyrptocurrency ta samu tagomashin farfaɗowa, bayan kamfanoni da cibiyoyi irin su PayPal sun amince su bar kwastomomin su yin hada-hadar kuɗaɗen.
Sannan kuma za su amince wa kwastomomin su na Birtaniya su saya ko su sayar da ‘bitcoin’ da sauran nau’ukan ƙwandalolin ‘cryptocurrency’ daga wannan mako da aka shiga a yau.