Ƴan bindiga sun sace tsohon shugaban hukumar NBC da iyalansa a Bakori jihar Katsina

0

Ƴan bindiga sun sace tsohon shugaban hukumar NBC da ya shugabanci ofisoshin hukumar da ke shiyyar Sokoto da Maiduguri, Ahmed AbdulKadir a gidansa da ke Bakori, jihar Katsina.

Majiya ta sanar mana cewa dama duk karshen mako ya kan zo Bakori daga Katsina wajen daya daga cikin matan sa dake Bakori.

An ce maharan sun afka masa cikin gida da karfe 9 na dare ne suka arce da shi da ƴar sa Laila da wasu mutum uku.

A cikin makon jiya an yi garkuwa da iyalan wani ɗan majalisar Katsina Aminu Kurami a garin Bakori.

Mahara sun sace matarsa da ƴaƴan sa biyu.

Share.

game da Author