Sanatan dake wakiltar Kaduna ta tsakiya ya roki Uba Sani ya roki yayan jam’iyyar da ba su ga maciji a tsakanin su, su zo a hada kai domin jam’iyyar APC ta yi nasara a zaben kananan hukumomi dake tafe.
Sanata Sani ya bayyana haka a taron yayan jam’iyyar APC da aka yi a Kaduna ranar Litinin.
” Dole sai mun yayyafe wa juna mun dawo mun hada kan mu wuri daya domin samun nasara a zaben da ke tafe. Ba zai yiwu ace kai ya rarrabu ba sannan kuma mu yi nasara, dole sai mun hada kai an yayyafe idan muna so mu samu nasara.
Haka shima kakakin majalisar dokokin Kaduna, Yusuf Zailani shima kira yayi ga yayan jam’iyyar su yi hakuri da matsalolin da aka fada a ciki a baya a dawo a hada kai domin jam’iyyar ta yi nasara a zaben kananan hukumomin da za ayi ranar Asabar.
Hukumar Zabe ta jihar Kaduna na ci gaba da shiri domin tunkarar zabukan kananan hukumomin dake tafe ranar Asabar a jihar.
kamar yadda ta gudanar a 2018, a wannan karon ma za a yi zaben ne ta hanyar naurar zabe mai kwakwalwa.
Tuni har gwamnati ta shigo da na’urorin zaben sannan kuma hukumar na horas da ma’aikatan wucin gadin da za su yi mata aiki ranar zaben.
Discussion about this post